16
Jan
Daga WAKILINMU A ƙoƙarin ƙara kusantar gwamnati da al’umma tare da inganta ayyukan jinƙai, Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ayyana ƙudurinta na kai ziyara dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar domin tattauna matsaloli da damuwar jama’a, tare da lalubo hanyoyin magance su. Shugaban ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta raba wa manema labarai. Ya yi bayanin ne jim kaɗan bayan ƙaddamar da rabon babura guda 50 da aka bayar kyauta ga jama’ar yankin…
