16
Jan
Hukumomin tsaro a ƙasar Mali sun kama wani boka da ya kira kansa masani bayan ya yi alƙawarin zai taimaka wa ƙasar su lashe Gasar Kofin ƙasashen Afrika (AFCON) ta hanyar sihiri, inda ya karɓi fiye da yuro dubu talatin da uku daga jama’a. An kama mutumin ne bayan fitar Mali daga gasar. Rahotanni sun bayyana cewa mutumin, mai suna Sinayogo, an kama shi ne a Bamako ranar Asabar, kwana guda bayan Senegal ta doke Mali da ci 1-0 a wasan kwata fainal na AFCON 2025. Kafin haka, Sinayogo ya riƙa bayyana kansa a matsayin marabout, wato boka na gargajiya,…
