ukarofi

12662 Posts
An kashe fiye da ‘yan bindiga 200 a Jihar Kogi

An kashe fiye da ‘yan bindiga 200 a Jihar Kogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumomin Nijeriya sun ce jami’an tsaro sun kashe fiye da ‘yan bindiga 200 a wani "gaggarumin samamen haɗin gwiwa" da aka gudanar a jihar Kogi da ke tsakiyar Nijeriya, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile matsalar rashin tsaro a ƙasar. ‘Yan sanda sun kuma kama wasu da ba a fayyace adadinsu ba, wasu daga cikin su sun ji raunuka daban-daban sakamakon musayar wuta da aka samu. Ana kuma bin sawun sauran 'yan bindigan da suka tsere, kamar yadda hukumomin suka faɗi. Kwamishinan harkokin yaɗa labarai na Jihar Kogi,…
Read More
Yadda jami’an tsaro suka daƙile wani harin ’yan bindiga a Gombe

Yadda jami’an tsaro suka daƙile wani harin ’yan bindiga a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jami’an tsaro sun samu nasarar daƙile wani harin ’yan bindiga da ake zargi an yi yunƙurin kaiwa garin Guda Lamido, da ke yankin Kashere a ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe huɗu na asubahin ranar Talata, 13 ga Janairu, 2026, bayan da aka samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga da dama sun yi yunƙurin kutsa kai cikin ƙauyen domin kai hari. Bayan samun rahoton ne jami’an rundunar ’yan sanda tare da ’yan sintiri da mafarauta suka yi gaggawar kai ɗauki wurin, inda suka tari hanzarin maharan, lamarin…
Read More
CAN ta ƙaryata zargin ta’addanci da ake yi wa gwamnan Bauchi 

CAN ta ƙaryata zargin ta’addanci da ake yi wa gwamnan Bauchi 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya  (CAN) reshen jihar Bauchi ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa Gwamna Bala Mohammed da wasu daga cikin muƙarrabansa na ɗaukar nauyin ta'addanci, inda suka ce zargin babu tushe kuma yana da manufa ta siyasa. A cikin wata sanarwa da shugaban CAN, Reɓ. Abraham Dimeus, da Sakataren ƙungiyar, Reɓ. Matthew Laslimbo suka sanya hannu, ƙungiyar ta bayyana cewa zargin ya kasance sharri ne da aka yi don ɓata sunan gwamnan da kuma jihar Bauchi. ƙungiyar ta kuma zargi cewa waɗannan ƙorafe-ƙorafen ɓangare ne na shirin abokan gaba na…
Read More
Dattawan Jihar Ribas sun yi gargaɗi kan yunƙurin tsige Gwamna Fubara 

Dattawan Jihar Ribas sun yi gargaɗi kan yunƙurin tsige Gwamna Fubara 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar Dattawa da shugabannin Jihar Ribas, ta nuna damuwa kan sanarwar neman tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Ordu. Shugaban riƙon ƙungiyar, Dr. Gabriel Toby, wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar ne, ya soki wannan yunkuri a cikin wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal ranar Asabar. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa 'yan majalisar dokokin jihar Ribas sun bayyana shirinsu na tsige Fubara bayan wani taron gaggawa da suka yi ranar Laraba. Mr Toby ya ja hankalin cewa tsigewa wani muhimmin tsari ne a kundin tsarin mulki, bai  kamata…
Read More
NAPTIP ta ceto yara 58 daga cikin 300 da suka bace a Jihar Benuwe

NAPTIP ta ceto yara 58 daga cikin 300 da suka bace a Jihar Benuwe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Hana Safarar mutane na ƙasa NAPTIP a ranar Talata ta bayyana cewa jami’an ta sun ceto wasu yara 58 daga cikin 300 ɗin da suka ɓace a jihar Benuwe Shugaban shiyyar Hukumar dake jihar Benuwe Gloria Bai ta sanar da haka a taron da ta yi da manema labarai a garin Makurdi. Gloria wace shugaban ayyukka na Hukumar Yusuf Abdul ya wakilce ta a taron ya ce Hukumar ta ceto wadannan yara a lotukata daban-daban. Ta ce tun bayan ɓacewar yaran Hukumar a watan Mayu 2025 ta fara gudanar da bincike. Gloria ta…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka sace mutum 32 a Jihar Kaduna

Yadda ‘yan bindiga suka sace mutum 32 a Jihar Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ana fargabar wasu 'yan bindiga sun yi awon-gaba da mutum 32 ciki har da ƙananan yara tare da kashe mutum 1 a wani hari da suka kai garin Kadagen Kauru da ke ƙaramar Hukumar Kauru ta jihar Kaduna. Harin na zuwa ne bayan wani makamancinsa da 'yan bindiga suka kai a watan da ya gabata, inda ake zargin sun sace mutum 85 a garin Kabari da ke makwabtaka da garin na Kadagen Kauru, bayan ga jerin hare-hare da suka kai wasu daga cikin ƙauyukan yankin. Bayanai sun tabbatar da cewa ana ci gaba da…
Read More
Kasafin 2026: An ware biliyan N1.07 don gyaran gidan Tinubu da Shettima

Kasafin 2026: An ware biliyan N1.07 don gyaran gidan Tinubu da Shettima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 1.07 domin gyaran gidajen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a kasafin kuɗin 2026, lamarin da ya sanya adadin kuɗin da aka ware don gyaran gidajen su cikin shekara uku ya kai Naira biliyan 18.4, in ji rahoton Daily Trust. Haka kuma, Hukumar EFCC, wadda kuɗinta ke ƙarƙashin sashen fadar shugaban ƙasa a kasafin, ta shirya kashe Naira biliyan 3.2 a bana domin tsaftace ofisoshinta da da kuma abinci da kayan shaƙatawa. Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi na 2026 a w zaman haɗin gwiwar…
Read More
Real Madrid: Tafiyar Alonso da zuwan Arbeloa

Real Madrid: Tafiyar Alonso da zuwan Arbeloa

Kungiyar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta Real Madrid ta sanar da korar kocinta Xabi Alonso sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon da ƙungiyar ke samu a kakar wasan bana, tare da naxa Arbeloa a matsayin sabon koci domin jagorantar tawagar a sauran wasannin da suka rage. An ga wasu bidiyoyi da suka yaɗu, inda Kylian Mbappe ke yi wa abokan wasansa wata alamar da ke nuna yana son su bar fili bayan kammala wasan da ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na kofin Spanish Super Cup da aka buga a Saudiyya. A cikin bidiyon an ga yadda Xabi Alonso ya…
Read More
Barcelona ta lashe Spanish Super Cup na karo na 16

Barcelona ta lashe Spanish Super Cup na karo na 16

Barcelona ta lashe Spanish Super Cup na biyu a jere na 16 jimilla, bayan doke Real Madrid 3-2 a wasan El Clasico na farko a bana da suka kara a Saudiyya ranar Lahadi. Kenan ƙungiyar Camp Nou ta lashe wasa na 10 a jere a dukkan fafata, rabon da a doke ta tun cikin watan Nuwamba da Chelsea ta samu nasara a Champions League. Wasan El Clasico na huɗu da a jere da Hansi Flick ya doke Real Madrid - biyu a Super Cup da kuma Copa del Rey - Haka kuma Barcelona ce kan gaba a teburin La Liga…
Read More
Michael Carrick ya karɓi ragamar riƙon ƙwarya a Manchester United

Michael Carrick ya karɓi ragamar riƙon ƙwarya a Manchester United

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta tabbatar da nadin tsohon ɗan wasanta, Michael Carrick, a matsayin koci na riƙon ƙwarya har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. Fitaccen masani kan kasuwar ’yan wasa, Fabrizio Romano, ne ya fara bayyana labarin, inda ya ce an kammala yarjejeniyar baki tun ranar Litinin, sannan yanzu an cimma matsaya gaba daya, har da batun tawagar mataimakan da Carrick zai zo da su. A cewar rahotanni, tsohon ɗan wasan tsakiya na Man United zai zo da wasu amintattun mataimaka, ciki har da wani tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar, domin taimaka masa wajen jagorantar…
Read More