17
Jan
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima za su kashe jimillar kuɗi har Naira biliyan 9.36 a shekarar 2026 wajen tafiye-tafiye na cikin gida da na waje, tare da kuɗin ciyarwa da hidimar abinci, kamar yadda ke ƙunshe a cikin daftarin kasafin kuɗin shekarar da gwamnati ta gabatar. Wannan bayanai na cikin takardun kasafi da Ofishin Kasafin Kuɗin Tarayya ya fitar, bayan da Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 58.18 a gaban Majalisar Dokoki a ranar 19 ga Disamba, 2025. A jawabinsa lokacin gabatar da kasafin, Shugaban ƙasa ya bayyana…
