18
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce magoya bayansa a cikin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na fuskantar matsin lamba kan shirin gwamnan na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC. A kan haka, jagoran na jam’iyyar NNPP, ya buƙace su da su rattaɓa hannun domin rage tashin hankalin da suka tsincin kan nasu a ciki. Kwankwaso ya yi waɗannan makalaman ne a ranar Talata cikin wani sakon bidiyo da mai taimaka masa na kafafen sada zumunta, Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ana ganin yunƙurin Gwamna Abba na shiga APC…
