ukarofi

12662 Posts
Fim ɗin ‘Kitso Da Kwarkwata’: Yadda sunansa ya bi shi tun farkon farawa

Fim ɗin ‘Kitso Da Kwarkwata’: Yadda sunansa ya bi shi tun farkon farawa

Daga MUKHTAR YAKUBU  A kwanakin baya kaɗan da suka gabata ne aka kammala ɗaukar wani sabon fim mai suna 'Kitso da Kwarkwata', wanda kamfanin shirya fina-finai mai suna Goldin Pin Multimedia ya ɗauki nauyin shiryawa. Mustapha Adam Muhammad shi ne ya zamo jagoran shirin, inda aka yi amfani da jarumai masu yawa – kama daga tsofaffin jarumai da kuma sababbi.  Fim ne mai dogon zango, wanda da zarar an kammala shi za a nuna shi a manyan gidajen talabijin da kuma manhajar YouTube da sauran manhajojin kallo. Kamar yadda binciken Blueprint Manhaja ya tabbatar ma na, farkon shirya fim ɗin…
Read More
Yadda fim ɗin ‘Behind The Scenes’ ya zama fim mafi kawo kuɗi a Nollywood

Yadda fim ɗin ‘Behind The Scenes’ ya zama fim mafi kawo kuɗi a Nollywood

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fitacciyar jarumar finafinai kuma furodusa a Nollywood, Funke Akindele, ta kafa wani sabon tarihi a masana’antar shirya fina-finai a Afrika bayan da sabon fim ɗinta mai suna ‘Behind The Scenes’ ya zarce kuɗin shiga na Naira biliyan biyu a gidajen kallo. Rahotanni sun nuna cewa, fim ɗin ya zama na farko a tarihin Nollywood da ya taba kai wa wannan mataki a Afrika, lamarin da ya mayar da Funke Akindele babbar darakta kuma mai shirya fim mafi samun kuɗi a nahiyar baki ɗaya. A ranar Lahadi, 12 ga Janairu, 2025, Funke Akindele ta tabbatar da wannan…
Read More
An rantsar da shugabannin ƙungiyar ‘yan fim ta KAFIGAN reshen Jihar Kano

An rantsar da shugabannin ƙungiyar ‘yan fim ta KAFIGAN reshen Jihar Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU  An rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar 'yan fim ta KAFIGAN reshen Jihar Kano waɗanda za su jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa. A daren ranar Asabar 10 ga Janairun nan ne aka yi taron rantsar da sabbin shugabannin a ɗakin taro na Meenat Eɓent Center dake Lodge Road a Unguwar Nassarawa GRA cikin garin Kano. Taron wanda ya samu halartar dubbun jama'a daga sassa daban-daban na ƙasar nan, an fara shi ne da misalin ƙarfe 7 na dare. Tun da farko da yake jawabi a wajen taron, Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar Alhaji Ismaila Na'abba…
Read More
Noel: Matashin da ke jinin al’ada duk wata kamar mace

Noel: Matashin da ke jinin al’ada duk wata kamar mace

Shafin Al’ajabi ya saba binciko abubuwan da ke ban mamaki, labaran da ke ɗaure kan mutane, tare da buɗe idanu kan halittun Allah da ke wuce hasashen kwakwalwa. A wannan karo, mun kawo muku labarin wani matashi daga ƙasar Philippines wanda rayuwarsa ta cika da sirri mai nauyi, sirrin da ya ɗauki shekaru yana ɓoyewa cikin zuciya. Noel, wani matashi daga garin Batangas, ya fara fuskantar abin da bai taɓa zato ba tun yana kusan shekara 12. Kowane wata, na tsawon kwanaki, sai ya riƙa zubar da jini kamar yadda mata ke yi a lokacin al’ada. Ba wai ƙananan ɗigo…
Read More
Gasar rage farashin fetur ta ƙara ƙarfi yayin da gidajen mai ke sayarwa ƙasa da Dangote

Gasar rage farashin fetur ta ƙara ƙarfi yayin da gidajen mai ke sayarwa ƙasa da Dangote

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kasuwar man fetur a Nijeriya na fuskantar sabon yanayi mai zafi, yayin da wasu gidajen mai suka fara sayar da man fetur a ƙasa da Naira 739 kan kowace lita – farashin da matatar Dangote ta ayyana a matsayin 'ma-fari'. Wannan ya nuna cewa gasa tsakanin ’yan kasuwa tana ƙara ƙarfi, abin da ke kawo sauƙi ga masu saye, amma yana jefa ’yan kasuwa cikin matsin lamba. Binciken da majiyar Blueprint Manhaja ta gudanar ya nuna cewa matakin da matatar Dangote ta ɗauka a watan Disamba na rage farashin fetur daga kusan N900 zuwa N739 kan…
Read More
Nijeriya da Dubai sun cimma yarjejeniyar soke haraji kan kayayyaki 13,000

Nijeriya da Dubai sun cimma yarjejeniyar soke haraji kan kayayyaki 13,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cimma wata babbar yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wadda ta tanadi soke haraji kan fiye da kayayyaki 13,000 domin bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen biyu da kuma haɓaka fitar da kayayyakin da ba na mai ba daga Nijeriya. A cewar wata takarda da Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya ta fitar, Nijeriya ta soke haraji kan kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga UAE, yayin da UAE ta cire haraji kan kayayyaki 7,315 daga Nijeriya, ƙarƙashin Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki ta Nijeriya da…
Read More
Gwamnatin Yobe ta fara gina kasuwanni domin farfaɗo da tattalin arziki

Gwamnatin Yobe ta fara gina kasuwanni domin farfaɗo da tattalin arziki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jihar Yobe na ɗaukar matakai masu ƙarfi na sake gina tattalin arziki bayan shekaru na rikicin Boko Haram, inda gwamnatin jihar ke aiwatar da shirin gina kasuwanni na zamani a sassa daban-daban domin bunƙasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi. Wata tawagar ’yan jarida daga gida da ƙasashen waje na rangaɗi a halin yanzu domin duba waɗannan sabbin kasuwanni, tare da ganin da idonsu yadda ake aza tubalin farfaɗo da rayuwar al’umma da rikici ya daɗe yana gallaza wa. Rangadin, wanda gwamnatin jihar ta shirya, ya nuna muhimmancin shirin da Gwamna Mai Mala Buni ke…
Read More
Gwamnatin Kano ta horar tare da tallafa wa matasa 2,260

Gwamnatin Kano ta horar tare da tallafa wa matasa 2,260

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala horaswa tare da tallafa wa matasa 2,260 a fannoni daban-daban na sana’o’i, a wani yunƙuri na bunƙasa samar da ayyukan yi da ƙarfafa dogaro da kai a faɗin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin bikin kammala horaswa da rabon tallafi ga waɗanda suka amfana da shirin, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano. Gwamnan ya bayyana bikin a matsayin sabon babi ga matasan da suka ci gajiyar shirin, yana mai buƙatar su zama masu amfani ga tattalin arzikin jihar ta hanyar amfani da kwarewar da…
Read More
Saƙon 2026: Kungiyar Arewa ta buƙaci shugabanni su dawo kan tafarkin gaskiya

Saƙon 2026: Kungiyar Arewa ta buƙaci shugabanni su dawo kan tafarkin gaskiya

Daga DAUDA USMAN a Legas Kungiyar Al'ummar Arewa ta 'Arewa Community Forum' da ke Legas ta aika da saƙo ga shugabanni da dattijan Arewa a farkon sabuwar shekarar 2026, inda ta buƙaci su kare muradun jama’a, su kuma cika alƙawuran da suka ɗauka a lokacin hawa mulki. A cikin saƙon da Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar, Alhaji Dr. Ibrahim Tanko, ya rattaba wa hannu, an bayyana cewa shugabannin yanzu sun taka rawa wajen raunana zaman lafiya, daƙile ci gaba, da kuma jefa Nijeriya cikin matsin lambar ƙasashen waje. Ya yi nuni da matakin da Amurka ta ɗauka na ayyana Nujeriya…
Read More
Gidauniyar Manar El-Huda ta horas da mata kan kyautata zamantakewar aure

Gidauniyar Manar El-Huda ta horas da mata kan kyautata zamantakewar aure

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana mata a matsayin ginshiƙin tarbiyyar al’umma, inda kashi 80 cikin 100 na tarbiyyar yara ke fitowa daga hannunsu, yayin da iyaye maza ke bayar da kaso 20 cikin 100. Wannan ne ya sa ake buƙatar uwa ta gari domin a samu zuri’a mai cike da kyakkyawar tarbiyya. Babban malamin addinin Musulunci, Farfesa Umar Sani Fagge, ne ya bayyana hakan a yayin jawabinsa a taron yaye mata da aka horas da su kan tarbiyyar zaman aure a ƙarƙashin Gidauniyar Manar El-Huda. Taron ya gudana ne a makarantar firamare ta Fagge a ranar Asabar. Farfesa…
Read More