ukarofi

12735 Posts
Tanimu ya buƙaci Gwamnatin Gombe ta yi gini don tunawa da Janar Abacha

Tanimu ya buƙaci Gwamnatin Gombe ta yi gini don tunawa da Janar Abacha

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Jagoran al’umma kuma jakadan zaman lafiya, kwamared Maishanu Abubakar Tanimu, ya buƙaci Gwamnatin Jihar Gombe da ta karrama marigayi Janar Sani Abacha ta hanyar sanya sunansa a wani muhimmin gini ko babbar hanya, domin tunawa da rawar da ya taka wajen ƙirƙiro da jihar. Da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, Tanimu ya ce al’ummar jihar na da haƙƙin tunawa da Janar Abacha, domin a zamanin sa ne a shekarar 1996 aka kafa Jihar Gombe daga tsohuwar Jihar Bauchi. Ya bayyana cewa da ba don wannan mataki na tarihi ba, da Gombe ba ta…
Read More
Ranar Malamai Ta Duniya: AUSUSS ta koka wa Gwamnan Kano

Ranar Malamai Ta Duniya: AUSUSS ta koka wa Gwamnan Kano

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/kudu Ranar 5 ga watan Oktoba na kowacce shekara, ranace da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin murnar da yabawa malaman makarantu akan iri ƙoƙarin da suke yi wajen samar da illimi ga al'umma. Da nufin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen tafiyar da sana'ar tasu domin samun al'umma ta gari. Kazalika ranace da ake gudanar da bukukuwa da gabatar da jawabai kan wasu sabbin dabarun Koyarwa ko wata matsala, inda hukumomin illimi kan taro da jami'an gwamnati duk dan nunawa malaman muhimmanci wannan rana har ma da gabatar da wasu yan koke koken dan daukar matakin da…
Read More
Al’ummar Gidan Mantau da Mai Farin Kai a Katsina sun karɓi tallafin kuɗi daga hukumar CSDA

Al’ummar Gidan Mantau da Mai Farin Kai a Katsina sun karɓi tallafin kuɗi daga hukumar CSDA

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Al’ummar garuruwan Gidan Mantau da Mai Farin Kai na ƙaramar hukumar Malumfashi sun karɓi horo da takardun kuɗi (cheques) daga hukumar inganta rayuwar al’umma ta Jihar Katsina (CSDA), domin gudanar da muhimman ayyukan al’umma da gwamnatin jihar ta yi musu alƙawari. An gudanar da wannan taro ne a ɗakin taro na sakatariyar ƙaramar hukumar Malumfashi. A jawabin sa Ko’odinetan shirin KT-CARES na jihar Katsina, Alhaji Nafi’u Muhammad, wanda Alhaji Abdullahi Hudu Ingawa ya wakilta, ya jajanta wa al’ummar garuruwan bisa iftila’in da suka fuskanta sakamakon harin ’yan bindiga. Ya bayyana cewa manufar shirin KT-CARES ita…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta gina tashar rediyon FM

Gwamnatin Katsina za ta gina tashar rediyon FM

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Katsina ta ware Naira miliyan 366 wajen samar da tashar FM rediyo a jihar. Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu Dr Salisu Bala zango ya sanar da haka a lokacin da yake kare kasafin kuɗin ma'aikatar sa na 2026 a gaban ma'aikatan kasafin kuɗi da tsare-tsare na jihar. Ya bayyana cewa har an sami amincewar kafa gidan rediyon ga aka sa ran kafin ƙarshen shekaran nan an kammala aikin ginin. "Muna shirye shiryen tabbatar da ganin gidan rediyon ya fara aiki kafin kashen wannan shekara,"Inji Dr Bala Zango. Kwamishinan ya ce ana sa ran da…
Read More
Ina rubutu ne don yaɗa koyarwar addini da kyawawan al’adun Arewa – Fatima Bala 

Ina rubutu ne don yaɗa koyarwar addini da kyawawan al’adun Arewa – Fatima Bala 

"Na yi mamakin yadda littattafaina suka samu karɓuwa a sassan Nijeriya da Afirka" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Fatima Bala, wata marubuciya ce ýar Nijeriya da tauraronta ke haskawa, ba a Arewa kaɗai ba, har ma da wasu sassan Afirka. Kodayake rubutun da take yi da harshen Turanci ya fi mayar da hankali ne kan rayuwar ýan Arewa a Turai, musamman a ƙasar Kanada inda take zaune tare da iyalinta, amma muhimman darussan da take fitowa da su da suka shafi hukunce-hukuncen addini da tarbiyya, ya sa ta yi fice a tsakanin marubuta da manazarta a Nijeriya. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba…
Read More
Uwar Gidan Gwamnan Katsina ta ƙaddamar da rigakafin cutar ƙyanda

Uwar Gidan Gwamnan Katsina ta ƙaddamar da rigakafin cutar ƙyanda

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Uwar gidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Umar Raɗɗa, ta ƙaddamar da gangamin rigakafin cutar ƙyanda a Katsina, domin kare lafiyar yara a faɗin jihar. Da take jawabi a wajen ƙaddamarwar, Hajiya Zulaihat ta bayyana cewa cutar kyanda na daga cikin manyan matsalolin lafiya da ke addabar yara a ƙasar nan, wadda ka iya janyo nakasa ko ma mutuwa. Domin haka uwargidan Gwamnan ta yi kira ga iyaye maza da mata da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun karɓi wannan rigakafi domin inganta rayuwar su.” Ta ƙara da cewa dukkan jihohin Najeriya za su…
Read More
Katsina: Ban taɓa yin kwangila ba tun Ina gwamnati – Mustapha Inuwa

Katsina: Ban taɓa yin kwangila ba tun Ina gwamnati – Mustapha Inuwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina ‎Mustapha Inuwa ya ce tun lokacin gwamnatinMalam Umar Musa zuwa Aminu Bello Masari yake bada kwangila "amma ban taɓa yi da kaina ba ballantana ɗan wannan aikin," Inji shi.‎‎Dr Mustapha M Inuwa wanda tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina ne a lokacin gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar'adua da RT Hon Aminu Bello Masari yayi wannan bayani kan zargin da ake masa na kwangilan ruwan Yantumaki da na Dam ɗin Karamar hukumar Ɗanmusa wanda ya ƙaryata hakan. Wasu mutanen garin Ɗanmusa suke zarginsa da cewa gwamnatin baya ta bashi kwangilar aikin Dam ɗin Ɗanmusa da na Kawo…
Read More
Zargin auren dole: Iyali sun wanke Sarkin Mafara tare da neman afuwarsa

Zargin auren dole: Iyali sun wanke Sarkin Mafara tare da neman afuwarsa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Mahaifan Maryam wadda tun da farko ita da Mahaifiyarta suka zargi Sarkin Talatan Mafara, Dakta Bello Mohammed Barmo a Kihar Zamfara da yin amfani da ƙarfin ikon sa wajen aurar da Maryam ga wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Mi’awiyya sun wanke Basaraken daga zargin da suka yi masa cewar yana da hannu a kan lamarin. Malam Umar Musa wanda kawun Maryam ne ya jagoranci tawagar Iyalan zuwa fadar Sarkin a yau ranar Talata ya bayyana hakan a gaban Sarkin. A cewarsa, sun je fadar Sarkin ne domin su wanke shi da zargin da Mahaifiyar…
Read More
Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira ga gwamnati da ta ƙara yawan jami’an tsaro a Kusada

Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira ga gwamnati da ta ƙara yawan jami’an tsaro a Kusada

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sakamakon sulhu da 'yan bindiga suka yi da alummomi a ƙananan hukumomin da su kai ta fama da rashin tsaro a jihar a yanzu dai zaman lafiya ya fara samuwa a yankunan. To sai dai akwai fargaban cewa wasu yan bindiga sun baro waɗannan ƙananan hukumomi zuwa wasu da suke zaune lafiya. A kan haka ne Majalissar Dakoki ta jihar katsina, tayi kira zuwa ga sashen zartaswa da a ƙara jami’an tsaro a Magama,Sabarawa,Mazoji, Jeri,Duza,Tsohuwarmai Jigira da Kofa dake ƙaramar hukumar Kusada. A zaman majalisar ɗan majalissa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kusada, Hon. Ghali Garba…
Read More
Malam Aliyu Ƙanƙara ya zama farfesa

Malam Aliyu Ƙanƙara ya zama farfesa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shahararren marubucin Hausa, wanda ya yi fice wajen bincike kan rayuwa da waƙoƙin marigayi Dakta Mamman Shata Katsina, Dakta Aliyu Ibrahim Ƙanƙara ya samu ci gaba a fannin ilimi, inda ya zama Farfesa na farko a fannin ilimin da ya shafi halittun duwatsu (Geology) a Jami'ar Tarayya da ke Dutsin-ma, Jihar Katsina. Muƙaddashin shugaban jami'ar, Farfesa Aminu Ado ne ya sanar da wannan ci gaba a yayin taron musamman karo na 135 na hukumar zartarwa na jami'ar. A yayin taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na sashin nazarin noma da ke babbar harabar jami'ar,…
Read More