ukarofi

12735 Posts
Rayuwa jarrabawa ce, ba kodayaushe karatun da mutum ya yi yake fitowa a tambayoyin ba – Shamsiyya Ibrahim Barde

Rayuwa jarrabawa ce, ba kodayaushe karatun da mutum ya yi yake fitowa a tambayoyin ba – Shamsiyya Ibrahim Barde

"Rashin ƙwaƙƙwaran abin yi bayan aure ne babban ƙalubalen mata" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Mata na ba da gagarumar gudunmawa ga al'amuran da suka shafi cigaban al'umma, ta ɓangarori daban-daban. Daga ciki akwai mata da ke ba da gudunmawa a fagen harkar hidimar jama'a tare da ƙungiyoyi masu zaman kansu, suna gudanar da ayyukan jinƙai waɗanda jama'a da dama ke farinciki da su. Wannan agaji da taimako da ake bai wa waɗanda ke cikin halin tagayyara shi ya ja hankalin matashiya, Shamsiyya Ibrahim Barde, ýar garin Potiskum a Jihar Yobe ta shiga aikin hidimar al'umma, musamman bayan fitintinun da aka…
Read More
2027: So na ke na ɗora daga inda Gwamna Sule ya tsaya – Farfesa Haruna

2027: So na ke na ɗora daga inda Gwamna Sule ya tsaya – Farfesa Haruna

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Dan takarar kujerar gwamnan Jihar Nasarawa a zaɓen shekarar 2027 dake tafe a inuwar jam'iyyar APC, Injiniya Farfesa Sani Muhammad Haruna yace ba shakka bai wa shiyar Kudancin jihar damar fito da gwamnan jihar da zai gaji gwamna Abdullahi Sule a 2027 zai tabbatar da adalci da zaman lafiya da kuma fahimtar juna a jihar baki ɗaya. Ɗan takaran ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin mu John Wada a gidan sa dake G.R.A a birnin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jiya Litinin. A cewar sa sanin kowa ne…
Read More
Ka kuwa san muhimmancin lokaci?

Ka kuwa san muhimmancin lokaci?

Dag BILKISU YUSUF ALI Ka taɓa jin kamar kwanakin ka suna tafiya cikin sauri, amma kai ba ka cimma komai ba? Wannan shi ne alamar rashin amfani da lokaci yadda ya kamata matsalar da take shafar miliyoyin mutane a duniya, tana jawo damuwa, rashin nasara, da wahalhalu marar misaltuwa. Lokaci shi ne mafi mahimmancin albarkatun da ɗan Adam ya ke da shi. Kowa na da sa’a 24 a rana, amma yadda mutum ke amfani da wannan lokaci shi ke bambanta tsakanin nasara da rashin nasara a rayuwa. Lokaci abu ne mai tafiya ba tare da dakatawa ba. Ba za a…
Read More
Ƙungiyar NUT ta karrama gwamna Raɗɗa

Ƙungiyar NUT ta karrama gwamna Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Mallam Dikko Umar Raɗɗa ya lashe kyautar karramawa ta ƙasa kan gyaran fannin Ilimi. Gwamnan ya samu kyautar zinariya ta girmamawa kan ci gaban ilimi da jituwa da malamai daga ƙungiyar Malaman makaranta ta ƙasa (NUT), saboda gagarumin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo a ɓangaren ilimi da kuma kulawar da yake nunawa ga walwalar malamai. An miƙa wannan karramawa ne a ranar Lahadi, yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2025 da aka gudanar a Eagle Square, Abuja, ƙarƙashin taken “Sake Fassara Koyarwa a Matsayin Sana’ar Haɗin Kai.” A jawabinsa bayan…
Read More
Ƙungiyar Dangin Juna Afrika ta raba wa marasa ƙarfi 120 abinci a Yobe

Ƙungiyar Dangin Juna Afrika ta raba wa marasa ƙarfi 120 abinci a Yobe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ƙungiyar jin ƙai ta dangin juna Afrika Initiative (DJAI) ta gudanar da rabon kayan abinci ga mutane 120 masu rauni da marasa ƙarfi a masarautun Fika da Potiskum da ke Jihar Yobe. A wani ɓangare na shirin ta na shekara-shekara na taimako. Da yake jawabi a fadar mai martaba sarkin Fika da ta Mai Potiskum, shugaban ƙungiyar na ƙasa, QS Usman BK, ya ce shirin na cikin ƙoƙarin rage wa marasa galihu raɗaɗin rayuwa da kuma ƙarfafa halin sadaka da taimako a tsakanin membobin ƙungiyar. Ya bayyana cewa membobin ƙungiyar na tara kuɗi a…
Read More
Shugabar Jami’ar Nasarawa ta buƙaci haɗin kai a fannin kasuwanci don cigaban duniya

Shugabar Jami’ar Nasarawa ta buƙaci haɗin kai a fannin kasuwanci don cigaban duniya

Daga JOHN WADA a Keffi Shugabar Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman, ta bayyana buƙatar ƙasashen duniya su rungumi sabbin hanyoyin ci gaba da ba wai kawai suna kawo riba ba, amma suna ɗorewa, domin fuskantar manyan ƙalubale irin su sauyin yanayi, ƙarancin abinci, da raguwar albarkatun ƙasa da ke addabar ƙasashe daban-daban na duniya. Farfesar ta bayyana haka ne a wajen buɗe taron kwana uku na farko na ƙasa da ƙasa kan ƙirƙire Ƙirƙire da nuna kayayyaki , wanda sashen nazarin kasuwanci (Entrepreneurship Studies) na jami’ar ya shirya. Taken taron shi ne: “Kirkire-Kirkire a Kasuwanci…
Read More
Yan sanda sun haɗa gwiwa da kamfanin ƙarafa na NAK don taron wayar da kan masu sana’ar gwangwan

Yan sanda sun haɗa gwiwa da kamfanin ƙarafa na NAK don taron wayar da kan masu sana’ar gwangwan

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Taron an shirya shi ne akan faɗakar da masu sana'ar gwangwan kan hatsarin ɗaukar ababen fashewa a Katsina. 'Yan sandan sun gabatar da wasu daga cikin ababen fashewa dake barazana da rayuwar al’umma a yayin taron. Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina tare da haɗin gwiwar Kamfanin NAK Steel Rolling Processing Mill Limited da Ƙungiyar Masu Sana’ar gwangwani na Najeriya (NASWDEN) suka shirya wani taron wayar da kai da faɗakarwa ga masu sana’ar gwangwani da sauran masu sana’ar ƙarafa. Da yake jawabi a lokacin taron, mai magana da yawun 'yan sanda na Jihar Katsina PPRO…
Read More
Gwamnonin Arewa na da kuɗin ɗaukar nauyin tsaro – Gwamna Sule

Gwamnonin Arewa na da kuɗin ɗaukar nauyin tsaro – Gwamna Sule

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce, yanzu gwamnatocin jihohi a Nijeriya su na da wadatattun kuɗaɗe fiye da yadda suke da su a shekarun baya. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa wajibi ne a karkatar da kuɗin zuwa sassan da za su iya sauya tattalin arzikin ƙasar nan. Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron Northern Nigeria Inɓestment and Industrialisation Summit (NNIIS) 2025 da aka gudanar a Abuja. Ya ce, kuɗin da ake rabawa tsakanin matakai uku na gwamnati sun ninka sau huɗu sakamakon gyare-gyaren da Shugaba Bola Tinubu ya…
Read More
An yi kira ga Gwamna Raɗɗa ya gyara hanyar Joɓawa a ƙaramar hukumar Mani

An yi kira ga Gwamna Raɗɗa ya gyara hanyar Joɓawa a ƙaramar hukumar Mani

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Al'ummar yankin Joɓawa da ke ƙaramar hukumar Mani, na yin kira ga Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa da ya gyara masu hanyar su da ta ratsa garuruwa fiye da 20. Da yake magana da manema labarai a madadin alummar garin malam Lawan Liman Joɓawa ya bayyana cewa yanzu haka ko mota bata shiga garin su, sai dai ayi amfani da mashina ko jakai ko kuma amalanke. Lawan Liman ya ce ko marar lafiya ke gare su, saboda rashin kyan hanya, kafin akai shi Asibiti ya rasa ranshi. Hanyar dai an yi ta ne…
Read More
Otedola ya buƙaci Tinubu ya tona asirin masu badaƙalar tallafin mai

Otedola ya buƙaci Tinubu ya tona asirin masu badaƙalar tallafin mai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hamshaƙin attajirin nan na Nijeriya, Femi Otedola, ya buƙaci shugaban aasa Bola Ahmed Tinubu da ya bayyana cikakken rahoton kwamitin da Aigboje Aig-Imoukhuede ya jagoranta kan yadda ake badaƙala kan tsarin tallafin man fetur da aka yi a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan. Otedola, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Lahadin da ta gabata, ya nace cewa ‘yan Nijeriya sun cancanci sanin gaskiya game da waɗanda suka wawure baitul malin ƙasar ƙarƙashin shirin Asusun Tallafawa Man Fetur (PSF), wanda ya karkatar da biliyoyin daloli a ƙasar. A cikin sanarwar, Femi Otedola…
Read More