06
Oct
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ranar Litinin ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara ƙaimi wajen mayar da Nijeriya sahun gaba wajen zuba jari a nahiyar Afirka ta hanyar tattaunawa da manyan ’yan kasuw masu zuba jari, Hakeem Belo-Osagie na Metis Capital da Bayo Ogunlesi na Global Infrastructure Partners & BlackRock. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, babban taron, wanda aka gudanar a Legas, ya mayar da hankali ne kan buɗe manyan ayyukan zuba jari a fannin mai, iskar gas, da kayayyakin more rayuwa a Nijeriya, muhimman wuraren da gwamnatin ke kallo a matsayin gunshiƙan ci…
