ukarofi

12735 Posts
Kungiyoyin ma’aikatan jinya a Kaduna sun yaba wa gwamna Uba Sani

Kungiyoyin ma’aikatan jinya a Kaduna sun yaba wa gwamna Uba Sani

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A wani taron manema labarai da suka kira a ofishin Kwamishinan Yaɗa Labarai, gamayyar ƙungiyoyin Ma'aikatan Lafiya da ke aiki a jihar Kaduna, sun yaba wa Gwamna Uba Sani bisa gyara da inganta harkar kiwon lafiya a duk faɗin jihar. Gamayyar ma'aikatan lafiyar, waɗanda suka haɗa da ƙungiyar Likitoci ta ƙasa, reshen jihar Kaduna, da ta asibitin koyarwa na Barau Dikko, ƙungiyar ma'aikatan jinya da Unguwar-zoma (NANNM), ma'aikatan lafiya fannin binciken cututtuka, tare da dukkan ƙungiyoyin harkar lafiya da ke Kaduna, sun jinjjna wa Gwamnan bisa irin kulawar da ya ke bayarwa ga harkar lafiya ta…
Read More
Za mu ci gaba da kare muradun Arewa – ACF

Za mu ci gaba da kare muradun Arewa – ACF

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A yayin take shirin gudanar da bikin cika shekaru 25 da kafuwa, ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (AFC) ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen kare kai da kuma inganta muradu da ƙimar Arewa. Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, Alhaji Dalhatu Wazirin Dutse, ya tabbatar da haka a lokacin da ya jagoranci sauran mambobin ƙungiyar ta ACF a ziyarar ban girma da suka kai wa Gwamna Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Talata. Alhaji Dalhatu ya sanar da mai masaukinsu cewa an kafa dandalin ne a shekara ta 2000, wanda…
Read More
Kungiyar ’yan kasuwar Bichi ta gana da shugaban Cibiyar Al-furqan

Kungiyar ’yan kasuwar Bichi ta gana da shugaban Cibiyar Al-furqan

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ci gaba da kai ziyarar girmamawa da nufin tattaro shawarwari da za su haɓaka kasuwanci a Karamar Hukumar Bichi, ƙungiyar 'Yan Kasuwa ta Bichi Traders Multi-Purpose Cooperatiɓe Society Limited ta samu ganawa da Shugaban sashen Ilimi na Cibiyar Al-furƙan Foundation Kano, kuma na’ibin limamin Masallacin Juma’a na FCE (T) Bichi, Malam Ashiru Abdulkadir Yakasai. Malam Ashiru Yakasai, ya yi musu fatan alheri da jan hankali, akan su kasance masu haƙuri da tsoron Allah a cikin kasuwancinsu kuma su guji shirya abinda zai gurbata tunanin matasa da sauran al’umma, kamar yadda Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta…
Read More
PDP ta ce ba za ta sanya wa ‘ya’yanta da ke alaƙa da APC takunkumi ba a yanzu 

PDP ta ce ba za ta sanya wa ‘ya’yanta da ke alaƙa da APC takunkumi ba a yanzu 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar PDP ta amince cewa wasu daga cikin ‘ya’yanta na alaƙa da Jam’iyyar APC mai mulki amma ta ce ta zaɓi kada ta sanya musu takunkumi a yanzu, inda ta fifita haɗin kai da kwanciyar hankali gabanin babban taronta na ƙasa da kuma babban zaɓen 2027. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Debo Ologunagba, Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar na ƙasa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata a Abuja yayin da yake jawabi ga manema labarai kan shirye-shiryen jam’iyyar na zaɓen fidda gwani na babban taronta na ƙasa da aka shirya…
Read More
Gwamnatin Tinubu na dukan ‘yan Nijeriya da ɗanyen kara – Mustapha Tinubu 

Gwamnatin Tinubu na dukan ‘yan Nijeriya da ɗanyen kara – Mustapha Tinubu 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da cewa mutum ne mai son cigaban al'umma  amma sai dai ba shi da mashawarta a gwamnatinsa masu kishi, da a ce akwai irinsu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso jagoran Kwankwasiyya a kusa da shi da talaka ya yi sambarka saboda zai kawo gyara. Hon. Mustapha Muhammad Tinubu (Chiranchi) jigo a tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai bayan ɗaurin aure da aka yi na 'ya'yansa. Mustapha Tinubu wanda ya bayyana cewa sunansa da ake laƙanawa da Tinubu a ciki ya…
Read More
Shawarwari ga matasa masu shirin aure (3)

Shawarwari ga matasa masu shirin aure (3)

Assalamu alaikum. Abu na uku da na ke son nuni da shi, shi ne muhimmancin sassauci da yafe wa juna, duk da cewa sassauci ba abu ne da ke da kyau a dukkan lokuta ba na rayuwa ba, to amma mafi kyawun sassauci da yafuwa akan yi shi ne a rayuwa ta aure. Don kuwa, a matsayinku na sabbin amare da angwaye, za su ci daba da fahimtar junanku da kuma ɗabi'un juna kusan kullum. To lalle kada irin waɗannan sabbin abubuwa su kashe muku gwiwa, don kuwa babu wani mutum a duniyan nan (a halin yanzu) da ya cika…
Read More
Laifin talaka ne ko na shugabanni?

Laifin talaka ne ko na shugabanni?

Duk wahalar da talakawa ke sha a Nigeriya ba damuwar akasarin shugabanni bane tunda har yau cewa su ke yi za su tallafa da kuɗi da abinci na wucin gadi. Sauran lokacin kuma ba a san wa zai taimaka ba. Duk da haka maganar talaka da malamai laifin mu ne mu gyara halayen mu, sun manta sace dukiyar talaka da rufe kan iyakokin ƙasa sun hana ayyukan yi da shigo da kayan buƙata da karya darajar naira da cire tallafin mai su kaɗai suka rikita Nigeriya ko talaka na da hannu a kan su. Musamman 'yan arewa mu faɗawa juna…
Read More
Raba-gardama: Waƙoƙin zamani rubutattu ne ko na baka? 

Raba-gardama: Waƙoƙin zamani rubutattu ne ko na baka? 

Daga MD Asnanic 1.0 GABATARWA Masana, musamman na ɓangaren limin addinin Musulunci, sun bai wa sanin abu (ilimi) wasu darajoji hawa-hawa har zuwa hawa uku: daraja ta farko ita ce 'haƙƙul-yaƙini' (ilimin da ke tare da mutum yake jin sa a cikin jikinsa, kamar wata cuta da ke cin sa a cikin jikinsa), daraja ta biyu kuma 'aynul-yaƙini' (ilimin da ka gan shi muraratan, misali idan aka ce maka cuta kaza tana illa kaza kuma sai ka ga illar a jikin na tare da kai), daraja ta uku kuwa ita ce 'ilimul-yaƙini' (shi ne ilimin da za a faɗa maka…
Read More
NIJERIYA A 65: Ƙalubalen shugabanni da matasa

NIJERIYA A 65: Ƙalubalen shugabanni da matasa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ranar Laraba da ta gabata, ’yan Nijeriya suka gudanar da bikin murna da zagayowar Ranar Samun 'Yancin Kan ƙasa daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Ingila, wanda aka saba gabatarwa duk ranar ɗaya ga watan Oktoba. Babu shakka wannan babbar rana ce a tarihin Nijeriya, duba da irin ƙalubale da matsalolin da ƙasar ta daɗe tana gwagwarmayar tabbatar da su, tun daga 1960 shekarar da aka samu ’yancin kai. A kowace shekara, ranar samun 'yancin kai tana kasancewa rana ce mai muhimmanci sosai, domin tana tunatar da mu game da tarihi, jaruman da suka yi…
Read More
Gasar Kofin Duniya: FIFA na fuskantar matsin lamba a duniya bayan barazanar Trump

Gasar Kofin Duniya: FIFA na fuskantar matsin lamba a duniya bayan barazanar Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya jefa FIFA cikin ruɗanin siyasa, yana mai gargaɗin cewa zai iya ɗauke wasannin gasar kofin duniya daga garuruwan da Amurka ke karɓar baƙuncin da yake ganin ba su da tsaro kafin shekarar 2026. Barazanar shugaban Amurka mai ci ya haifar da tambayoyi game da ’yancin cin gashin kai na FIFA, da kwanciyar hankali a gasar, da kuma ko ƙwallon ƙafa ta duniya za ta iya jure tsoma bakin siyasa daga ofishin da ke da ƙarfi a duniya. Gasar cin kofin duniya ta 2026 za ta kasance mai tarihi, gasar farko ta faɗaɗa zuwa ƙungiyoyi 48…
Read More