ukarofi

12735 Posts
Ni da Chelsea mun zama abu ɗaya – Mourinho

Ni da Chelsea mun zama abu ɗaya – Mourinho

Tsohon kocin ƙungiyar Chelsea ta Ingila, Jose Mourinho wanda yanzu yake horar da ƙungiyar Benfica ya ce shi da ƙungiyar ta Stanford Bridge sun zama hanta da jini. Mourinho ya bayyana haka ne a ganawarsa da manema labarai kan shirye-shiryen da yake yi na jagorantar ƙungiyar Benfica ta ƙasar Portugal a wasan da za ta fafata da Chelsea na gasar zakarun turai a Ingila a ranar Talata. Sai dai ya ce a lokacin da ake tsaka da wasan, "zan jingine ƙaunar da yake yi wa Chelsea na minti 90 domin in fuskanci aikin da nake yi wa ƙungiyar Benfica." Ya…
Read More
Postecoglou ya nemi afuwar magoya bayan Forest

Postecoglou ya nemi afuwar magoya bayan Forest

Kocin Nottingham Forest, Ange Postecoglou ya buƙaci magoya baya su kara haƙuri, bayan da har yanzu bai ci wasa ba. Ranar Alhamis Forest za ta karɓi baƙuncin Midtjylland a Europa League a City Ground a karon farko tun bayan kusan shekara 30 rabon da ta shiga gasar zakarun Turai. Tsohon kocin Celtic da Tottenham ya maye gurbin Nuno Espirito Santo a watan Satumba, amma har yanzu bai ci wasa ba. Ya fara da shan kashi 3-0 a gidan Arsenal, sannan Swansea ta yi waje da su daga Carabao Cup da yin canjaras a Burnley da kuma a Real Betis a…
Read More
An naɗa Muhammad Musa Inyya shugaban gidan rediyo da talabijin na Hikima

An naɗa Muhammad Musa Inyya shugaban gidan rediyo da talabijin na Hikima

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano An naɗa Kwamred Muhammad Musa Inyya, tsohon Mataimakin Darakta a gidan rediyon Kano FM, kuma tsohon shugaban ƙungiyar Ma’aikatan Rediyo, Talabijin da Wasan Kwaikwayo ta ƙasa (NARTO) reshen Kano, a matsayin sabon Shugaban Gidan Rediyo da Talabijin na Hikima Rediyo. Naɗin ya biyo bayan sanarwar da Hon. Ibrahim Sha'aban Sharaɗa, mamallakin Hikima Rediyo kuma Shugaban Hukumar Zartarwa ta gidan rediyon ya fitar a tsakiyar makon da ya gabata. Sanarwar ta tabbatar da cewa Malam Inyya ya fara aiki a muƙaminsa tun ranar Laraba. A cewar Hon. Sha'aban Sharaɗa, tsohon ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kano…
Read More
Yadda ake samun ƙaruwar ɗariƙun sufaye a dalilin adawar wata ƙungiya — Sharif Haruna Abba

Yadda ake samun ƙaruwar ɗariƙun sufaye a dalilin adawar wata ƙungiya — Sharif Haruna Abba

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Daya daga cikin jagororin Sharifan Nijeriya, Alhaji Sharif Haruna Abba Garinali, ya bayyana cewa adawar da ƙungiyar Izala ta yi kan ɗariƙun sufaye ta ƙara bunƙasa su maimakon rage tasirinsu. Ya ce kafin wannan adawa, wasu daga cikin mabiya tariƙa ba sa tsayawa da ƙarfi wajen bin hanyarsu, amma bayan adawar, sai suka ƙara zurfafa ilimi da bincike tare da riƙe aƙidarsu da ƙarfi. Ya ƙara da cewa zuwan Izala ya ƙara haɓaka tarurrukan Maulidi, wanda yanzu suka fi yawa da bunƙasa fiye da da. Sharif Haruna ya jaddada cewa a tarihin Musulunci akwai irin…
Read More
Shaidar EFCC a kotu ya manta adadin kuɗaɗen da ya karɓa a hannun tsohon Gwamnan Taraba

Shaidar EFCC a kotu ya manta adadin kuɗaɗen da ya karɓa a hannun tsohon Gwamnan Taraba

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ranar Talata ne shari’ar tsohon gwamnan Jihar Taraba, Architect Darius Ishaku, da tsohon babban sakatare, Alhaji Bello Yero, ta ɗauki sabon salo a babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama, inda shaidar masu gabatar da ƙara na farko ya amince cewa bai san adadin kuɗaɗen da ake zargin ya karɓa a madadin tsohon gwamnan ba. Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) na gurfanar da Ishaku da Yero a gaban Mai Shari’a Sylɓanus Oriji kan tuhume-tuhume 15 masu lamba FCT/HC/CR/792/2024. Laifukan sun ci karo da laifukan da suka shafi cin amana, haɗa…
Read More
Boko Haram ta yanzu na iya zama wasan yara idan ba a ɗauki mataki ba – Obasanjo

Boko Haram ta yanzu na iya zama wasan yara idan ba a ɗauki mataki ba – Obasanjo

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya magantu kan ƙaruwar al’umma a Nijeriya, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a magance matsalar ba zai iya haifar da mummunar illa. A lokacin da yake jawabi a Sakkwato a wajen ƙaddamar da Cibiyar ICT ta Bakhita a Sakatariyar Katolika, tsohon Shugaban ya jaddada muhimmancin ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban aasa. "A shekara ta 2050, mutane irin su Sultan za su kasance a nan, ba ina addu'ar zama a nan shekaru 25 na gaba ba ne," inji Obasanjo. "Za mu fuskanci matsalar 'yan Nijeriya miliyan 400 da za…
Read More
Sakacin asibiti ne sanadin mutuwar ’yar jaridar Arise TV – Kwamared Onwubiko

Sakacin asibiti ne sanadin mutuwar ’yar jaridar Arise TV – Kwamared Onwubiko

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ko’odinetan ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta ƙasa (HURIWA), Kwamared Emmanuel Nnadozie Onwubiko, a ranar Talata, ya bayyana sakacin ma’aikatan babban asibitin Maitama Abuja a matsayin abin da ya taimaka wajen mutuwar ’yar jarida gidan talbijin na Arise, Somtochukwu Christelle Maduagwu. Tashar talabijin ta ARISE News ta sanar da rasuwar ma’aikaciyarta, Somtochukwu Christelle Maduagwu, wacce aka kashe a safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Satumba, 2025 sakamakon wani harin fashi da makami da aka kai a gidanta da ke unguwar Katampe a Abuja. A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, Onwubiko ya ce, dagewar da…
Read More
Nijeriya ta yi asarar biliyan N52.26 sakamakon ’yan damfara a 2024 – FCDO

Nijeriya ta yi asarar biliyan N52.26 sakamakon ’yan damfara a 2024 – FCDO

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bayanai daga Hukumar ’Yan Sanda ta ƙasa da ƙasa (Interpol) sun nuna cewa ayyukan zamba da damfara a Afirka sun ƙaru da kashi 3,000 a cikin 2024. Shugaban Hukumar Kula da Ci Gaban ƙasashe Rainon Afrika (FCDO) Sorrel Eɓans, wanda ya bayyana hakan a wajen ƙaddamar da Tsarin Daƙile Zamba na ISO37003:25 a ranar Talata a Abuja, ya ƙara da cewa Nijeriya ta yi asarar Naira Biliyan 52.26 sakamakon zamba a shekarar 2024. Adadin, a cewar Eɓans, yana nuna ƙaruwar kashi 295 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. "A cikin yanayin da…
Read More
NNPC ya rattaɓa hannu kan yarjejeniya ta samar da ɗanyen mai da Matatar Dangote

NNPC ya rattaɓa hannu kan yarjejeniya ta samar da ɗanyen mai da Matatar Dangote

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya ƙulla sabuwar yarjejeniya ta samar da ɗanyen mai da matatar man Dangote, inda zai ƙara samar da man na tsawon shekaru biyu a wani mataki da ake sa ran zai ƙarfafa shirin Gwamnatin Tarayya na "ɗanyen mai Naira". Yarjejeniyar wacce aka kammala a watan Satumba, kamfanin mai na gwamnati zai samar wa matatar mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana kago biyar-biyar na ɗanyen mai a watan Satumba da Oktoban 2025, a cewar kakakin NNPC, Andy Odeh. Odeh, wanda ya tabbatar da tsarin a cikin martanin saƙon rubutu…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ƙarin N32,000 ga ’yan fansho

Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ƙarin N32,000 ga ’yan fansho

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Tsarin Fansho ta ƙasa (PTAD) ta sanar da fara aiwatar da ƙarin kuɗaɗen fansho da aka amince da shi kwanan nan ba jimawa. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, hukumar ta ce, karin N32,000, ga masu karɓar fansho da suka cancanta, an tabbatar da shi ne a cikin tsarin biyan fansho na watan Satumba na 2025. A cewar PTAD, ci gaban ya biyo bayan fitar da wani ɓangare na naira miliyan 420.188 daga cikin kuɗaɗen gaggawa na Naira Biliyan 45 da shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a…
Read More