ukarofi

12738 Posts
ADMUN ta gudanar da taro na ƙasa karo na 12 a Gombe

ADMUN ta gudanar da taro na ƙasa karo na 12 a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ƙungiyar mata Musulmai masu larurar ji a Najeriya ta ƙasa The Association of Deaf Muslim Women in Nigeria (ADMUN) ta gudanar da taron ta na ƙasa karo na 12 a Jihar Gombe, tare da kira mai ƙarfi ga hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su samar da tsare-tsare da zasu haɗa kowa da kowa, domin tallafawa mata Musulmi kurame a faɗin ƙasar nan. An gudanar da taron na kwanaki uku ne mai taken: “Ƙarfafa Mata Musulmi Kurame ta Hanyar Imani, Ilimi da Haɗin Kai,” tare da haɗin gwiwar ƙungiyar haɗakar mata Musulmi ta…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da taron jin ra’ayoyin al’umma a mazaɓu 361 da ke jihar

Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da taron jin ra’ayoyin al’umma a mazaɓu 361 da ke jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya bada umurni ga dukkan zaɓaɓɓun wakilai da su saurari buƙatun al'ummar su wanda haka zai taimaka wa gwamnati a shirye shiryen da take na sauya fasalin kasafin kuɗin jihar na shekara ta 2026. Mataimakin gwamnan jihar malam Faruk Lawal Jobe wanda ya wakilci gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da shirin a mazabar sa ta Ƙanƙara A da B dake a cikin ƙaramar hukumar Ƙanƙara. A jawabinsa na buɗe taron mataimakin gwamnan, ya bayyana cewa" Gwamnan Jihar katsina shi ne, ya bada umarnin cewa" dukkan wanda aka zaɓa ko mai muƙamin gwamnati…
Read More
Babu alaƙa babu cin hanci: Yadda Gwamnan Kano ya karɓi rahoton Kwamishinan Sufuri kan belin dillalin ƙwaya

Babu alaƙa babu cin hanci: Yadda Gwamnan Kano ya karɓi rahoton Kwamishinan Sufuri kan belin dillalin ƙwaya

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton wani kwamitin bincike kan rawar da Kwamishinan Sufuri na Jihar, Alhaji Ibrahim Namadi Dala, ya taka a bayar da belin wani da ake zargin da safarar ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a rana Talata, an bayyana cewa Gwamna Yusuf ya karɓi rahoton ne a fadar gwamnati daga Sakataran Gwamnati, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, wanda shi ne shugaban kwamitin. A yayin gabatar da rahoton, Sakataran Gwamnati ya bayyana muhimman abubuwan da…
Read More
Gwamnan Kano ya bai wa jami’an tsaro umarnin kamo ‘yan dabar da suka halaka hadiminsa

Gwamnan Kano ya bai wa jami’an tsaro umarnin kamo ‘yan dabar da suka halaka hadiminsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bai wa jami’an tsaro umarnin Kamo duk wanda yake da hannu a sanadiyyar mutuwar hadiminsa Sadiq Gentle. “Ina matuƙar alhini game da rasuwar Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman a ma’aikatar tarihi da al’adu ta Jihar Kano, wanda ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a wani mummunan harin da wasu da ake kyautata zaton ƴan daba ne suka kai a baya-bayan nan”. A cikin saƙon ta’aziyyar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikewa Manhaja Blueprint, gwamna Yusuf ya…
Read More
Wa ya rage bai mutu ba a Gaza?

Wa ya rage bai mutu ba a Gaza?

Haƙiƙa babbar tambaya ce a idanu cewa wa ya rage bai mutu ba a Zirin Gaza? Amma gaskiyar lamarin in ka ga mutum na rayuwa yanzu a Gaza to kawai jiran ko-ta-kwana ya ke yi za ta kwana ko dai za a kwana da shi a lahira. Duk bayanin da wani mai sharhi zai yi sai dai ya zama kwatance kasancewar shiga Gaza ga mai daukar rahotanni ba abu ba ne mai sauƙi. Hatta masu raba kayan agaji ma kan fuskanci kisa balle a je ga wani mai ɗaukar labaru musamman na kafar labarum da Isra’ila ke ɗauka na jin…
Read More
Gwamnatin Katsina ta rufe asibitoci masu zaman kansu guda biyu saboda rashin cika ƙa’idoji

Gwamnatin Katsina ta rufe asibitoci masu zaman kansu guda biyu saboda rashin cika ƙa’idoji

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnati ta ɗauki matakin rufe asibitocin ne bisa zargin gudanar da ayyukan jinya ba tare da cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa na buɗe cibiyoyin lafiya, da karya dokokin kula da lafiyar jama’a. Kwamishinan harkokin lafiya Hon Musa Adamu Funtua ya sanar da ɗaukan wannan mataki a lokacin da ya fara ziyarar gani da ido a asibitoci masu zaman kansu a jihar. Cibiyoyin lafiyar da aka rufe sun haɗa da, G-11 Medicine Store , Dental Emergency da Ɗan Ƙofa Medicine Store, bayan da aka gano suna gudanar da ayyukan jinya ba tare da cika ƙa’idojin rajista…
Read More
Kwamitin kula da ƙananan hukumomi da masarautu na majalisar Katsina ya gudanar da zama na musamman

Kwamitin kula da ƙananan hukumomi da masarautu na majalisar Katsina ya gudanar da zama na musamman

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A jawabinsa a wajen taron, shugaban kwamitin, Honarabul Ibrahim Ɗanjuma Machika, ya bayyana cewa manufar taron ita ce ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin kwamitin da shugabannin ƙananan hukumomi, tare da tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban al’ummar su da jihar musamman a matakin ƙananan hukumomi. Ya ƙara da cewa, taron na da muhimmanci sosai domin bayar da dama ga ‘yan majalisar su fahimci matsaloli da ƙalubalen da shugabannin ƙananan hukumomi ke fuskanta a aikinsu na yau da kullum. "Wannan zama zai taimaka wajen tsara hanyoyin magance matsaloli da kuma inganta gudanar da ayyukan…
Read More
NS-TA&G2 ga Akanta Janar na Nasarawa: Ka daina siyasa ko ka ajiye muƙamin ka

NS-TA&G2 ga Akanta Janar na Nasarawa: Ka daina siyasa ko ka ajiye muƙamin ka

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Wata ƙungiya da ake kira NS-TA&G2 dake Jihar Nasarawa ta buƙaci akanta janar na gwamnatin Jihar Nasarawa Hon. Musa Ahmed Mohammed ya ajiye wannan muƙamin sa na mai sa ido a kuɗaɗen gwamnatin jihar idan yana sha'awar tsunduma cikin siyasa ko fitowa takarar kujerar gwamnan jihar. Ƙunkiyar tayi kiran ne ga akanta janar ɗin ta bakin Lazarus Salaki a lokacin da suke zantawa da manema labarai a makon da ake ciki a birnin Lafiya babbar fadar gwamnatin jihar. Yace kiran ya zama wajibi idan akayi la'akari da yadda duk da wata umurni na musamman…
Read More
Sarkin Daura ya tabbatar da sarautar Sarkin Gabas ga shugaban NLC reshen Jihar Katsina

Sarkin Daura ya tabbatar da sarautar Sarkin Gabas ga shugaban NLC reshen Jihar Katsina

‎Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina ‎Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar, ya tabbatar wa shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen Jihar Katsina, Kwamared Hussaini Hamisu Yanduma, da sarautar Sarkin Gabas na Daura.‎‎Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar ɗauke da sa hannun Danejin Daura, Alhaji Abdulmuminu Salihu, a madadin Majalisar Masarautar.‎‎Kwamared Hussaini Hamisu Yanduma, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta ƙasa, ya sami wannan sarauta ne saboda irin gudummuwar da yake bayarwa wajen ci gaban Masarautar Daura, da Jihar Katsina da kuma Nijeriya baki ɗaya a cewar masarautar.‎Masarautar ta bayyana Alhaji Hussaini Hamisu…
Read More
Gwamnatin Katsina ta raba sama da Naira miliyan 11 ga waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa

Gwamnatin Katsina ta raba sama da Naira miliyan 11 ga waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta raba tallafin kuɗi har naira miliyan 11 da dubu 250 ga iyalan da harin ƴan bindiga ya shafa a ƙananan hukumomin Bakori da Faskari. Babban mataimaki na musamman ga gwamna kan lamuran waɗanda harin ƴan bindiga ya shafa da ƴan gudun hijira, Hon. Sa’idu Ibrahim Danja (Kogunan Jibia), ne ya jagoranci rabon kuɗaɗen a madadin gwamnati. Waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da iyalan waɗanda aka kashe, aka jikkata, aka sace ko waɗanda aka ƙona musu dukiyar su da dabbobin su. Gwamnati ta ba iyalan jami’an tsaro da suka mutu…
Read More