ukarofi

12738 Posts
Wani lokaci idan na kalli fim ina samun jigo a cikinsa – S. Reza

Wani lokaci idan na kalli fim ina samun jigo a cikinsa – S. Reza

"In dai da kayan ƙwalama a kusa na fi jin daɗin rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A wannan makon shafin Adabi ya yi gamo ne da wani matashin marubuci daga Jihar Binuwai, wanda ya daɗe yana ba da gudunmawa a harkar rubutun adabi, musamman a shafukan sada zumunta. Salis Reza ba ɓoyayye ba ne a tsakanin marubutan onlayin. Kodayake bai taɓa wallafa littafi ba, amma ya fitar da littattafai kimanin goma a onlayin. A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, S. Reza ya bayyana masa yadda aka yi sunan Reza ya bi shi.  MANHAJA: Mu fara da jin…
Read More
Kwamishinan sufuri na Kano Ibrahim Namadi ya yi murabus

Kwamishinan sufuri na Kano Ibrahim Namadi ya yi murabus

Daga USMAN KAROFI a Abuja Kwamishinan sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa jim kaɗan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Ɗanwawu. Wannan matakin ya kasance wani ɓangare na jajircewar gwamnatin jihar wajen tabbatar da gaskiya, adalci da ɗorewar amana a tsakanin jami’an gwamnati. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Namadi ya ce ya yanke shawarar sauka daga muƙamin sa ne…
Read More
Jami’an lafiya sun duba mata da ƙananan yara 67,262 a Dawakin Tofa

Jami’an lafiya sun duba mata da ƙananan yara 67,262 a Dawakin Tofa

Daga USMAN KAROFI a Abuja Jami’an lafiya a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa sun sami nasarar duba mata da ƙananan yara guda 67,262 a lokacin gudanar da makon mata da ƙananan yara da aka yi a yankin. Wannan bayanin ya fito ne daga shugabar sashen lafiyar matakin farko na yankin, Hajiya Balaraba B. Gambo, a wata hira da jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar. Hajiya Balaraba, ta bakin wakiliyarta Hajiya Talatu Sale, jami’ar kula da lafiyar mata da ƙananan yara, ta ce cikin waɗanda suka amfana akwai mata masu juna biyu 372 da aka basu magunguna, ƙananan yara 58,316 da kuma…
Read More
Sarkin Gombe ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu a matsayin Tafarkin Gombe

Sarkin Gombe ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu a matsayin Tafarkin Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI Gombe Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu, babban ɗan gidan sarauta daga zuriyar Bubayero, a matsayin Tafarkin Gombe ɗaya daga cikin sarautun da ake darajawa sosai a al’adun masarautar Hausa. Wannan naɗin ya zo ne a matsayin yabo da girmamawa kan gudummawar da Dakta Daudu ya bayar ga masarautar da ƙasa baki ɗaya. Dakta Daudu, wanda shi ne tsohon babban sakatare na tarayya, ya kasancce kwamishinan lafiya na farko a Jihar Gombe, daga baya ya riƙe muƙamin shugaban ma’aikata na Jihar Gombe sannan kafin daga baya…
Read More
Ruftawar bango: Mutane shida suka rasu a Katsina

Ruftawar bango: Mutane shida suka rasu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An wayi gari da kaɗuwa da samun labarin ruftawar wani bango a gidan wani magidanci mai suna Muhammad Sani Garba Dankama inda mutum shida suka rasa ran su wasu kuma suna asibiti. Bayan ɗaukewar ruwan sama bango ya faɗawa wata uwa da 'ya 'yan ta guda biyar inda nan take mutane shida suka riga mu gidan gaskiya. Kamar yadda mahaifin yaran Muhammad Sani Garba Dankama ya tabbatarwa da manema labarai cewa bayan an kammala ruwan sama da misalin ƙarfe 2:00am al'amari ya faru a unguwar Ƙofar Yamma cikin garin Dankama da ke ƙaramar hukumar Kaita…
Read More
Ɗan Majalisar Zamfara ya bai wa ɗaliban kiwon lafiya 61 jarin magunguna

Ɗan Majalisar Zamfara ya bai wa ɗaliban kiwon lafiya 61 jarin magunguna

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bunguɗu da Maru Hon. Abdulmalik Zubairu ya ɗauki nauyin ɗalibai 62 da suka yi karatu a fannonin kiwon lafiya daban-daban kuma har yanzu ba su da aikin yi da jari don fara sayar da magunguna a ƙauyukan su a faɗin mazaɓar sa. Ofishinsa ne ya ƙaddamar da aikin tare da haɗin gwiwar kwamitin kula da ci gaban al’umma da ƙarfafa wa (SCOCODE) a yau Talata. An bai wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin horarwa (Orientation training) kan yadda za su tafiyar da siyar da magungunan yadda ya kamata a…
Read More
Rashin Tsaro: ADC a Zamfara ta buƙaci Tinubu da Dauda su yi murabus

Rashin Tsaro: ADC a Zamfara ta buƙaci Tinubu da Dauda su yi murabus

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), reshen Jihar Zamfara, ta yi kira ga Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su yi murabus a matsayin gwamna da shugaban ƙasa idan har ba za su shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar ba. Shugaban jam’iyyar na jiha, Kwamared Kabiru Garba Gusau ne ya bayyana hakan, a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a yau Litinin, kan batutuwan da suka shafi ƙalubalen tsaro da durƙushewar tattalin arziki gaba ɗaya a jihar. Ya ce wanzuwar duk wani buri na gwamnati…
Read More
Wasu matasa sun buɗe kan wani jami’in tsaron da gatari a Jigawa

Wasu matasa sun buɗe kan wani jami’in tsaron da gatari a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Wasu matasa a kasuwar Shuwarin ta Jihar Jigawa yankin Ƙaramar Hukumar Kiyawa sun afka wa wani jami’in tsaro da sara da gatari da wasu muggan makamai a masayar dabbobi ta Shuwarin a daidai lokacin da wasu mutane su ka yi masa ihun ɓarawo. An ce waɗannan mutane da ake zargin ɓarayin ne sune suka yi masa ihun ɓarawo domin su kuɓutar da ɗan uwansu, shine mutane da ba su sani ba suka afka masa da suka sakamakon harbi da bindiga da shi wancan jami’in tsaro ya yi a kasuwar. Duba da wani yanayi na…
Read More
An buƙaci gwamnatin Katsina ta ƙarfafa tsaro a wasu ƙananan hukumomi

An buƙaci gwamnatin Katsina ta ƙarfafa tsaro a wasu ƙananan hukumomi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Malumfashi Hon. Aminu Ibrahim ya gabatar da ƙudirin, inda ya nemi abokan aikin shi na majalisa da su mara mashi baya, a tunatar da ɓangaren zartarwa na jihar Katsina domin ɗaukan matakin gaggawa. "Gwamnati ta ƙara ƙaimi tare da ƙarfafa tsaro, a yankunan Malumfashi da sauran ƙananan hukumomi dake fama da matsalar tsaro, dake a jihar,"inji ɗan majalisar. Ya bayyana cewa suna sane da ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina ke yi wajen samar da tsaro, amma dai a halin da ake ciki yanzu abubuwan sunyi ƙamari. Ɗan majalisar ya bada…
Read More
Hukumar kare muhalli ta gudanar da aikin tsafta a Katsina

Hukumar kare muhalli ta gudanar da aikin tsafta a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A ƙokarin ta na tsaftace babban birnin jihar, hukumar kare muhalli ta jihar (SEPA) ta gudanar da jerin ayyukan tsaftace muhalli kamar yadda ta saba. Shugaban hukumar Kabir Usman Amoga wanda ya jagoranci ma'aikatan sa wajen tsaftace manyan wurare a cikin garin Katsina ya bayyana cewa manufar hukumar ita ce tabbatar da tsaftar muhalli musamman a wannan lokaci na damina, domin kaucewa yaɗuwar cututtuka da kuma toshe hanyoyin ruwa. Ya tabbatar da cewa hukumar sa ba za ta gajiya ba wajen tsaftace manyan biranen jihar ta hanyar kwashe shara akai akai. Amoga ya yi kira…
Read More