ukarofi

12738 Posts
Kano ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyu miliyan biyar don yaƙi da gurɓatar yanayi

Kano ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyu miliyan biyar don yaƙi da gurɓatar yanayi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a jiya Lahadi ya ƙaddamar da kamfen na dasa bishiyu miliyan biyar na 2025 a Dausayin Yanbawa da ke ƙaramar hukumar Makoɗa. Wannan shiri na da nufin magance illolin sauyin yanayi, inganta muhalli, da kuma ƙarfafa ɗorewar lafiyar muhalli. Yayin ƙaddamarwar, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar samar da bishiyu a faɗin Jihar Kano domin inganta sauyin yanayi. Ya bayyana cewa farfaɗo da dausayin, wanda aka yi watsi da shi tun bayan da aka kafa shi a 1972, wani ɓangare ne na dabarun inganta sauyin yanayi da…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya taya sabbin hakimai da masarautar Katsina ta naɗa murna

Gwamna Raɗɗa ya taya sabbin hakimai da masarautar Katsina ta naɗa murna

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wannan bayanin ya fito daga babban jami'in yaɗa labarai na gwamna, Muhammad kaula. Gwamnan ya bayyana naɗin ya nuna yadda masarautar Katsina ta ke lura da cancanta,ƙwazo da mutumtaka kafin bada sarauta. Gwamnan ya bayyana sabbin hakiman a matsayin ya'yan masarautar da suka sadaukar da rayuwar wajen aikin gwamnati da cigaban al'umma. Gwamnan yayi fatan za suyi amfani da matsayin da Allah ya basu wajan kyautatawa al'ummar su da daga darajar gundumar su da jihar baki ɗaya. Sabbin hakiman sun haɗa da Sanusi Kabir Usman ƙani ne ga Sarkin Katsina,a matsayin (Karshin Katsina) Hakimin Shinkafi…
Read More
Kansila ya ɗauki mataimaka na musamman guda 10 a Katsina

Kansila ya ɗauki mataimaka na musamman guda 10 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hon Kabir Ɗalhatu (shooter)na mazaɓar Galadima a ƙaramar hukumar kankiya ya ƙaddamar da waɗannan mataimakan na musamman tare da bada tallafi na kayan sana'a ga mata su 40 domin ƙarfafa sana'ar su. Mataimakan na musamman da kansilan ya ɗauka za su taimaka masa a wajen bada shawarwari akan abinda ya shafi mazaɓar da sauran hidimomin siyasa. Sannan mata guda 40 da aka ba tallafin sana'a an basu waken suya domin su inganta sana'ar su ta awara da suke gudanarwa yau da kullum domin su dogara da kansu. Bugu da ƙari Hon. Kabir Ɗalhatu ya bada…
Read More
Shirin Boska Pain-Free Day ya kai wa fiye da mutane 5,000 Tallafin Lafiya Kyauta a Yola

Shirin Boska Pain-Free Day ya kai wa fiye da mutane 5,000 Tallafin Lafiya Kyauta a Yola

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya, kamfanin Dexa Medica, masu ƙera maganin saukar zafi na Boska, sun bayar da kulawar lafiya kyauta ga fiye da mutane 5,000 a Yola, Abuja, Kano, Onitsha, Ibadan, Legas da sauran wurare. A lokacin shirin Pain-Free Day, an gudanar da ayyukan lafiya kyauta da suka haɗa da duba lafiyar ido, gwajin hawan jini, gwajin sukarin jini, tausa na jiki, raba tabarau kyauta da kuma bayar da magunguna masu muhimmanci. Ana gudanar da wannan shiri duk wata a jihohi daban-daban domin inganta lafiyar al’umma tare da nuna godiya ga…
Read More
Uwargidan Gwamnan Zamfara ta taya Sarkin Katsinan Gusau murna bisa naɗinsa

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta taya Sarkin Katsinan Gusau murna bisa naɗinsa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta aike da wata tawaga mai ƙarfi wacce ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello bisa rasuwar mahaifinsa Marigayi Alhaji Ibrahim Bello tare da taya shi murnar naɗin da aka yi masa a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 16. Rabi’atu Yusuf babbar sakatariyar yaɗa labarai a ofishin Uwargidan Gwamnan ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Gusau yau Litinin. Tace, tawagar ta samu jagorancin Hajiya Larai Musa Lawal, inda ta miƙa saƙon ta’aziyyar Uwargidan…
Read More
Mata 1,000 a Gombe sun samu horon kasuwancin intanet

Mata 1,000 a Gombe sun samu horon kasuwancin intanet

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Kamfanin Shalele Enterprise da ke Jihar Gombe ya ƙaddamar da wani gagarumin shirin horar da mata 1,000 a jihar kan yadda za su gudanar da kasuwancin su ta hanyar amfani da kafar sadarwar intanet daga gidajen su. Da take jawabi a wajen ƙaddamar da shirin a jami'ar mallakar Jihar Gombe shugabar kamfanin, Hajjiya Maryam Ibrahim Jalo, ta bayyana cewa wannan shiri na nufin inganta rayuwar mata tare da ba su damar zama ’yan kasuwa masu dogaro da kansu ba tare da barin gidajen su ba. Maryam tace za su koyawa matan ne yadda za…
Read More
Wanda ake ƙara ya lakaɗa wa lauya duka a kotu kan yi masa tambayar ƙwaƙwaf

Wanda ake ƙara ya lakaɗa wa lauya duka a kotu kan yi masa tambayar ƙwaƙwaf

An ɗaure wani dattijo ɗan shekara 69 mai suna John Edward Njeru a gidan yari na tsawon kwana 1 saboda ya lakaɗa wa lauya duka yayin da lauyan ke gudanar da tambayoyi a cikin kotun. An bayar da rahoton cewa, tsohon Daraktan Ayyuka a ofishin 'yan sandan Kenya ya bar lauyan, Aleɗ Kimani, da munanan raunuka bayan da ya buge shi a ciki. An ce ya fusata cewa Kimani yana yi masa tambayoyi da yawa a cikin shari'ar da ya kasance mai shaida. An ce, ƙarar tana tsakanin wani dattijo ne wanda ya zargi wani ɗan kasuwa, Gabriel Njoroge Mbuthia…
Read More
Daulolin da Fulani suka yi nasarar kafawa a tarihi

Daulolin da Fulani suka yi nasarar kafawa a tarihi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mutanen Fula sun taimaka sun kafa dimokiraɗiyya da yawa na tarihin Islama kuma sun jagoranci yawancin Jihadi kamar Masina a ƙarni na 19. Masarautar Maasina wacce ake kira ‘Diina’ a Fulfulde, tare da asalin Larabci, an kafa ta ne ta hanyar jihadin Fulbe wanda Sheeku Aamadu ya jagoranta a 1818. Asalin masarautar Maasina a cikin Inner Delta na Niger shima ana samunsa a tawaye, a wannan karon kan Masarautar Bambara/Bamana na Segou, ikon siyasa wanda ke sarrafa yankin daga waje. Wannan jihadi ya sami karɓuwa ne daga abubuwan da suka faru a arewacin Nijeriya inda wani…
Read More
Mutuwar bazata da matakan kare kai

Mutuwar bazata da matakan kare kai

Fassara: AISHA ASAS Masanin cututtukan zuciya kuma Bishop na Cocin Anglican a Jihar Enugu, Farfesa Rt. Rev. Samuel Ike, ya bayyana cewa, babban dalilin da ke haddasa mutuwar gaggawa a Najeriya shi ne halin rayuwa mara tsafta, rashin samun kulawar lafiya cikin sauki, da kuma jahiltar alamomin barazana ga lafiya. Farfesan ya bayyana haka ne yayin wata lacca da aka gudanar a makarantar koyar da likitanci ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu (ESUT), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Enugu, mai taken: “Annobar Mutuwar Gaggawa a Cikin Al’umma: Me Za Mu Iya Yi?” A cewar Hukumar Labarai ta…
Read More
Yadda wasu jihohi suka kashe biliyan N102 wajen sayen kayan alatu a Kasafin 2025

Yadda wasu jihohi suka kashe biliyan N102 wajen sayen kayan alatu a Kasafin 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu jihohin Tarayyar Nijeriya guda 12 sun kashe jimillar zunzurutun kuɗi Naira Biliyan 102 a cikin kasafinsu na shekarar 2025, domin saka kayan alatu a gidajen gwamnati da sayen motocin alfarma, kamar yadda wani bincike da jaridar News Point Nigeria ta gudanar ya nuna. Kashe-kashe kuɗaɗen, wanda ya bayyana a rahoton ayyukan kasafin kuɗi na farkon shekara na jihohi, ya shafi kashe kuɗaɗe masu yawa a kan sayen motocin alfarma samfuran Toyota Prado, samfuran Jeep, motocin Hiluɗ, da manyan sedans kamar Toyota Camry da Corolla. Haka nan an haɗa su da adadi mai yawa don ginin…
Read More