04
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnonin jihohin Nijeriya da suka yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2007, sun buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali wajen kafa masana’antu. Sun ce kafa kamfanoni a ƙananan hukumomi ne zai taimaka wajen samar da ayyukan yi fiye da rabon tallafin N5,000. Tsofaffin gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan ganawa da suka yi da shugaban ƙasa a Abuja, ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion, a ranar Juma’a. Cif Igbinedion ya bayyana cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma noma tare da miƙa shawarwarinsu ga shugaban…
