ukarofi

12475 Posts
Aisha Lemu: Shin wace ce matar da ta taimaka wajen kafa IET, ta haɗa mata a ƙarƙashin FOMWAN?

Aisha Lemu: Shin wace ce matar da ta taimaka wajen kafa IET, ta haɗa mata a ƙarƙashin FOMWAN?

Daya daga cikin manyan buƙatun wannan zamani shi ne samar da ingantaccen bayani game da addinin Musulunci - Aisha Lemu  Daga AISHA ASAS  Shafin Gimbiya na wanonan makon ya kawo muku wata mace wadda Arewa da Najeriya suke da dalilin tunawa da ita. Mace ce da ta shafe fiye da rabin ƙarni tana aikin ilimi, Da’wah da kuma ƙarfafa mata, duk da yake ba ’yar Najeriya ba ce ta asali, ta zabi Najeriya ta zama gidanta, ta kuma sadaukar da mafi yawan rayuwarta wajen gina abubuwan da har yau ake ci gaba da amfana da su. Ita ce Hajiya Aisha…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe jami’in kuɗi na jami’ar NOUN a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe jami’in kuɗi na jami’ar NOUN a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jami'ar NOUN ta ƙasa ta Najeriya, NOUN, tana cikin jimami bayan kisan Malam Nasiru Marafa Gusau, wanda wasu da ake zargi 'yan ta'adda ne suka harbe shi yau Lahadi, yayin da yake komawa Abuja daga Gusau, Jihar Zamfara. A cewar wata sanarwa a hukumance wacce magatakarda kuma sakataren majalisar jami'ar, Oladipo Adetayo Ajayi ya sanya wa hannu, lamarin ya faru ne a yankin Tsafe zuwa Magazu yayin da Marafa ke kan hanyarsa ta komawa Abuja daga Gusau. "Jami'an da ke tare da shi sun sanar da hukumomin jami'ar game da harin". Shugaban jami'ar, a madadin…
Read More
Sanata Abdul’aziz Yar’adua ya miƙa makarantar Hajiya Dada ga hukumar Zakka da Waƙafi a Katsina

Sanata Abdul’aziz Yar’adua ya miƙa makarantar Hajiya Dada ga hukumar Zakka da Waƙafi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua da Hajiya Hafsat sun miƙa makarantar Mariganya Hajiya Dada ga hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina. Makarantar da Marigayiya Hajiya Dada ta gina, ana koyar da ilimin addinin Musulunci da na boko. Bayan rasuwarta, makarantar ta koma hannun Sanata Abdulaziz da Hajiya Hafsat, waɗanda daga baya suka yanke shawarar mayar da ita waƙafi ga iyayensu, Marigayi Alhaji Musa Yar’adua da Marigayiya Hajiya Dada, da kuma kawunansu. Hajiya Hafsat, wadda ta wakilci Sanata Abdulaziz, ta ce sun miƙa makarantar ga hukumar ne domin a ci gaba da kula da ita tare…
Read More
‘Yan sanda sun kama ɓarayin waya a Katsina

‘Yan sanda sun kama ɓarayin waya a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama mutane uku da ake zargi da hannu wajen kutsen gida, sata, karɓar kayan sata da haɗa baki wajen aikata laifi. Lamarin ya faru ne a Ƙofar Marusa, Katsina, inda wasu ’yan bindiga suka kutsa cikin wani gida da tsakar dare, suka sace wayoyin hannu daban-daban, turare da kuma zoben zinariya. Kamar yadda jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar,binciken ’yan sanda ya kai ga kama Abubakar Abbas, wanda aka fi sani da “Buti”, mai shekaru 24, inda aka same shi da…
Read More
Yadda masu tona kabari suka bayyana sirrin cire sassan jikin gawa don yin tsafin kuɗi

Yadda masu tona kabari suka bayyana sirrin cire sassan jikin gawa don yin tsafin kuɗi

Wani abin al’ajabi ya fito fili bayan wasu mutane da ake zargi da tona kaburbura da cire sassan jikin mamata domin yin tsafin neman kuɗi sun bayyana yadda suka shiga wannan mummunar sana’a, da kuma irin abubuwan da suke cirewa daga jikin gawawwaki. Wasu daga cikin mutane 10 da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta kama bisa zargin safarar sassan jikin ɗan adam domin yin tsafin neman kuɗi sun bayyana wa ’yan jarida yadda suke gudanar da wannan aiki. Mutanen sun bayyana cewa suna zuwa maƙabartar Musulmi da ke garuruwan Iseyin da Saki, inda suke tono sababbin kaburbura bayan an…
Read More
Tinubu ya farfaɗo da ’yan kasuwa da masu zuba jari – Fadar Shugaban ƙasa

Tinubu ya farfaɗo da ’yan kasuwa da masu zuba jari – Fadar Shugaban ƙasa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fadar Shugaban ƙasa ta ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun fara dawo da amincewar ’yan kasuwa da masu zuba jari ga yanayin kasuwanci a Nijeriya, tare da samar da sabbin damammaki ga ’yan kasuwa su bunƙasa. Mataimakiyar Fasaha kan Shirye-shiryen Ci Gaban Yankuna a Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa, Dakta Nafia Abdullahi, ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi yayin ƙaddamar da sabon shagon kasuwanci na Makib Estilo da aka buɗe a Central Area, Abuja. Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ce ta ƙaddamar da cibiyar kasuwancin. A wajen bikin,…
Read More
BUA da Dubai na duba sabbin hanyoyin faɗaɗa haɗin gwiwar tattalin arziki

BUA da Dubai na duba sabbin hanyoyin faɗaɗa haɗin gwiwar tattalin arziki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya karɓi baƙuncin Jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (wato Dubai) a Legas, Salem Aljaberi, inda suka tattauna hanyoyin ƙarfafa alaƙar Nijeriya da UAE tare da bunƙasa damar zuba jari da haɗin gwiwar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu. Rabiu ya bayyana farin cikinsa da karɓar babban jami’in diflomasiyyar UAE, yana mai yabawa ƙoƙarinsa wajen ƙara ɗaure dangantaka tsakanin Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. “Babban abin alfahari ne a gare ni na karɓi Mai Girma Salem Aljaberi, Jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Legas, a ofishina a yau,” inji Rabiu. Shugaban BUA ya ce…
Read More
Dangote ya kare matakin ƙara farashin mai duk da faɗuwar ɗanyen mai a duniya

Dangote ya kare matakin ƙara farashin mai duk da faɗuwar ɗanyen mai a duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Farashin man fetur ya ƙara tashi a sassan Nijeriya, inda litar man ta kai tsakanin N1,310 zuwa N1,400 a wasu wurare, yayin da Matatar Mai ta Dangote ta kare matakin da ta ɗauka na ci gaba da ƙara farashin man duk da raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya. Kamfanin ya danganta ƙarin farashin da tsadar ɗanyen man da ya riga ya saya tun farko, da kuma tsawon lokacin da ake ɗauka wajen kammala cinikin ɗanyen man, jigilar shi zuwa Nijeriya da kuma sauke shi a matatar. A halin yanzu, ana sayar da litar fetur kan…
Read More
Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya ta samar da Naira tiriliyan 1.83 a 2025

Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya ta samar da Naira tiriliyan 1.83 a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ma’aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku ta Nijeriya ta samar da kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 1.83 a shekarar 2025, lamarin da ke nuna ƙarin kashi 160 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira biliyan 700.79 da aka samu a shekarar 2023. Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja. Ministan ya ce ɓangaren harkokin ruwa na Nijeriya ya samu gagarumin sauyi cikin shekaru uku da suka gabata, tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa Ma’aikatar Harkokin Ruwa…
Read More
Yadda kotu ta yanke hukunci kan kisan mawaƙi Tupac bayan shafe shekaru ana bincike

Yadda kotu ta yanke hukunci kan kisan mawaƙi Tupac bayan shafe shekaru ana bincike

Daga AISHA ASAS  Bayan kusan shekaru 30 da aka kashe fitaccen mawakin rap na Amurka, Tupac Shakur, wani sabon babi ya bude a shari’ar mutuwarsa, bayan wata kotu a Las Vegas ta samu Duane “Keffe D” Davis da laifin kisan mawaƙin. Alƙalan kotun sun yanke hukuncin ne bayan sauraron shari’ar Davis, wanda ya kasance mutum daya tilo da aka gurfanar a gaban kotu kan kisan Tupac, wanda aka harbe shi a wani harin mota a Las Vegas a watan Satumbar 1996. Tupac ya rasu ne kwanaki shida bayan harin, yana da shekaru 25, kuma tsawon shekaru mutuwarsa ta kasance ɗaya…
Read More