08
Sep
Masu azancin magana kan ce “zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki.” Haƙiƙa, duk wani ci gaba da gwamnati ko masu hannu da shuni ko kuma ɗaidaikun mutane za su samar ba zai ɗore ba muddin babu zaman lafiya. Wannan ne ya sa duk wani ɗan ƙasa nagari ba ya da wata fata a ƙasarsa face samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. A ƙoƙarin samar da wannan zaman lafiya, gwamnati ta kafa hukumomi daban-daban kamar ’yan sanda, sojoji, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), Ciɓil Defence da sauransu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Haka kuma, gwamnati ta kafa Hukumar…
