ukarofi

12471 Posts
Dandalin shawara: Ina neman dabarun da zai sa saurayi ya dinga ba ni kuɗi ko ba yawa

Dandalin shawara: Ina neman dabarun da zai sa saurayi ya dinga ba ni kuɗi ko ba yawa

Daga AISHA ASAS  TAMBAYA: Assalamu alaikum. Aunty Aysha ya ki ke? Ya yara? Dan Allah shawara nake so a bani. Ina da saurayi, yana sona, ni ma kuma Ina son shi, ga shi iyaye na sun matsa min akan na fito da miji nai aure. Ni kuma na kasa gaya mai yanzu haka wancan sati akai auren ƙanwata yanzu sun ce in ban fito da miji nan da wata ɗaya ba, duk wanda suka zaɓa min shi zan aura. Ni kuma Ina son wancan, amma na kasa gaya mai, kuma shi wanda nake so bai ban kosisin kuɗi, bai taɓa…
Read More
Shaye-shaye da illolinsu ga matasa, lafiya da zamantakewa

Shaye-shaye da illolinsu ga matasa, lafiya da zamantakewa

Daga  DR. BILKISU YUSUF ALI Ci gaba daga makon da ya gabata. Kamar yadda muka faro a makon da ya gabata, shaye-shaye na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar al'ummomi da dama a duniya, musamman matasa. Matsalar tana shafar lafiyar jiki da ta kwakwalwa da ilimi da tattalin arziki da tsaro da zamantakewar al'umma. Wannan rubutu ta yi  nazari kan ma'anar shaye-shaye da nau'o'insu, abubuwan da ke jawo matasa shiga shaye-shaye, illolinsu ga lafiyar mutum da zamantakewa, tare da hanyoyin kariya da magance matsalar. Bincike ya nuna cewa haɗin gwiwar iyaye da malamai da shugabannin addini, gwamnati da al'umma…
Read More
Gwamnatin Kebbi ta rushe jagorancin hukumar zaɓe ta jihar

Gwamnatin Kebbi ta rushe jagorancin hukumar zaɓe ta jihar

Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris ta sanar da rushe jagorancin hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta jihar Kebbi (KESIEC). Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da da hannun sakataren gwamnatin jihar Alhaji Yakubu Bala Tafida ranar Talatar nan.Takardar ta bayyana cewa rushe jagorancin hukumar ya biyo bayan cikar wa'adin ta ne da ya yi daidai da ranar 18 ga watan Satumba na wannan shekarar ta 2026. Takardar ta bayyana cewa sai dai akwai mambobi biyu ta wa'adin aikin su bai cika ba su za su cigaba da aiki tare da sababbin da za…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira biliyan 828.646 a matsayin kasafin 2027

Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira biliyan 828.646 a matsayin kasafin 2027

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya gabatar da kasafin kuɗi Naira biliyan 828.646 na shekarar 2027 ga majalisar dokokin Katsina. Kasafin kuɗin da ya sanya ma suna 'Building your Future' ya bayyana cewar zai inganta rayuwar al'umma da tabbatar da kawo cigaba a birni da karkara da ke faɗin jihar. Gwamnan ya ce kasafin kuɗin shekara 2027 ya ragu da Naira biliyan 69.23. Haka kuma ya bayyana cewa kasafin kuɗin zai maida hankali akan Ilimi, Noma,Kiwon Lafiya da bunƙasa ƙasa. Malam Dikko Raɗɗa ya faɗa cewa gwamnatin sa zafi cika alƙawarin da yayi na kai ayyukan cigaba…
Read More
Abdulmutallaf Goya ya jagoranci kai samame maɓoyar ‘yan bindiga a Funtua

Abdulmutallaf Goya ya jagoranci kai samame maɓoyar ‘yan bindiga a Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙaramar hukumar Funtua, Hon. Abdulmutallab Jibril Sulaiman Goya, ya jagoranci samame na haɗin gwiwar jami’an tsaro zuwa wasu wurare da ake zargin ‘yan bindiga na amfani da su wajen fakewa da kuma kutsawa cikin garin Funtua. Samamen, wanda aka gudanar ya ƙunshi jami’an sojin ƙasa, da rundunar sojin sama, da ‘yan sanda, da MOPOL, da DSS, da FRSC, da C-Watch, da Vigilante da Civilian JTF, domin daƙile ayyukan masu aikata laifuka tare da ƙarfafa tsaron al’ummar yankin. Tawagar jami’an tsaron sun ratsa wasu muhimman wurare da suka haɗa da Cibauna, da Unguwar Biri, da…
Read More
Sanata Bello Mandiya ya rasu

Sanata Bello Mandiya ya rasu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Allah yayi wa tsohon Sanata Bello Mandiya rasuwa a daren litini a gidansa da ke Abuja. Babu wani bayani game da rasuwar sa. Kafin rasuwar Sanata Bello Mandiya ya wakilci shiyar Funtua a majalisar dattijai ƙarkashin jam'iyar APC a Jihar Katsina. Sanatan ya taɓa rike muƙamin shugaban ma'aikatan gidan gwamnnatin Katsina. Gwamna Dikko Raɗɗa ya ce ya kaɗu ƙwarai da ya sami labarin rasuwar Bello Mandiya. Ya bayana rasuwar sanatan a matsayin babban asara ba ma ga alummar jihar ba har ma ga ƙasa baki ɗaya. Yayi fatan Allah kai rahama ga kabarinsa.
Read More
Shinkafi ya sanya tsaro a matsayin babban ajandarsa idan ya lashe zaɓen gwamnan Zamfara

Shinkafi ya sanya tsaro a matsayin babban ajandarsa idan ya lashe zaɓen gwamnan Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan takarar gwamna a Jihar Zamfara a jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, Hon. Bilyaminu Yusuf Shinkafi, ya ce tsaron rayuka da dukiyoyi alumma zai zama babban abin da gwamnatinsa za ta sa a gaba idan aka zaɓe shi a 2027. Shinkafi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da aka gudanar a Kaduna. A cewarsa, rashin tsaro a Zamfara yana bukatar hanyar hadin gwiwa kuma ba za a iya barin gwamnati ita kaɗai ba. "Tsaro nauyi ne na haɗin gwiwa. Zan yi amfani da duk wata…
Read More
NDLEA za ta iya samar da zaman lafiya

NDLEA za ta iya samar da zaman lafiya

Masu azancin magana kan ce “zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki.” Haƙiƙa, duk wani ci gaba da gwamnati ko masu hannu da shuni ko kuma ɗaidaikun mutane za su samar ba zai ɗore ba muddin babu zaman lafiya. Wannan ne ya sa duk wani ɗan ƙasa nagari ba ya da wata fata a ƙasarsa face samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. A ƙoƙarin samar da wannan zaman lafiya, gwamnati ta kafa hukumomi daban-daban kamar ’yan sanda, sojoji, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), Ciɓil Defence da sauransu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Haka kuma, gwamnati ta kafa Hukumar…
Read More
Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Wannan wasiƙa an rubuta ta ne da zuciya ɗaya, da damuwa mai tsanani, da kuma fatan alheri. Ba da ƙiyayya ba, ba da tsinuwa ba, ba da zagi ba. Sai dai da ƙauna, nasiha, tunatarwa da kuma roƙo na gaskiya daga ɗan uwa zuwa ‘yan uwansa. Ina magana ne kai tsaye zuwa gare ku masu tuƙin ganganci – masu karya doka, masu sa rayuwar kansu da ta jama’a cikin hatsari a kullum. Direbobin motoci masu zaman kansu, masu kabu-kabu, musamman ’yan J5, Golf da Hiace. Masu adaidaita sahu da masu babur, musamman matasa. Da…
Read More
An gurfanar da ɗan Katsina kan zargin cin amanar ƙasa bisa cire allon tallar Tinubu

An gurfanar da ɗan Katsina kan zargin cin amanar ƙasa bisa cire allon tallar Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An tsare wani mazaunin Jihar Katsina, Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Nesta, tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin aikata laifin cin amanar ƙasa, bayan zargin cewa ya lalata allunan tallan siyasa da ke ɗauke da hoton Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Da farko ’yan sanda a Katsina sun gayyaci Sanda domin yi masa tambayoyi, kafin daga bisani su tsare shi bisa zargin cewa ya cire allunan tallan Shugaba Tinubu tare da kutse cikin Sakatariyar Jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, inda aka zarge shi da kwashe kuɗi har Naira miliyan 35.…
Read More