26
Aug
Shekaru 131 kenan tun bayan da al'ummar Kano suka tsinci kansu cikin mummunan yaƙin basasa sakamakon rikicin sarauta tsakanin gidan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi da gidan Sarkin Kano Muhammadu Bello, waɗanda dukkansu 'ya'yan Sarkin Kano Ibrahim Dabo ne. Masana tarihi sun bayyana wannan yaƙi a matsayin mafi muni da birnin Kano ya taɓa fuskanta. An rawaito cewa wani Bature da ya ziyarci Kano a lokacin ya ce, "Kano ta zama ƙasar jini saboda irin yawan jinin da aka zubar." Wannan yaƙi ya haifar da babbar asara ga rayuka, dukiyoyi da kuma tattalin arzikin birnin. Asalin rikicin: Bayan rasuwar Sarkin…
