Ba a ga watan Shawwal ba

Daga BASHIR ISAH

Kwamitin ganin wata na fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewar, ba a samu bayanin ganin jinjirin watan Shawwal ba.

Da wannan, ya tabbata bana Azumi 30 za a yi.

Tun farko, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ba da baki kan a nemi jinjirin watan Shawwal a ranar Asabar, 29 ga Ramadana, 1443 wanda ya yi daidai da 30 ga Afrilu, 2022.

Ganin watan Shawwal ne zai bai wa Musulmi damar kammala azumin Ramadana sannan a shiga bikin Sallah Ƙarama.

Ita ma Saudiyya, ta ba da sanarwar ba ta ga jinjirin watan Shawwal ba a ranar Asabar, don haka ita ma azumi 30 za ta yi.

Yanzu dai ya tabbata cewa al’ummar musulmi za a sake tashi da azumi ranar Lahadi, sannan Litinin mai zuwa a yi Ƙaramar Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *