An yi gasar Sinanci tsakanin ɗaliban jami’o’i a Nijeriya

Daga CMG HAUSA

A kwanan nan ne, cibiyar haɗin-gwiwa da musayar harsunan Sin da na ƙasashen waje da ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, suka haɗa kai da kwalejojin Confucius dake jami’o’in Namdi Azikiwe da na Legas dake Najeriya, don gudanar da gasar Sinanci ta ƙarshe ta kafar bidiyo ta ɗaliban jami’o’in ƙasa da ƙasa karo na 21 mai suna “Chinese Bridge”.

Babban jami’in kula da harkokin al’adu dake ofishin jakadancin Sin a Najeriya, Li Xuda ya bayyana cewa, harshen Sinanci, hanya ce da ake bi wajen mu’amala da fahimtar juna tsakanin al’ummu. Li na fatan masu sha’awar koyon Sinanci a Najeriya za su ƙara azama wajen koyonsa, don bada tasu gudummawa wajen haɓaka sada zumunta tsakanin ƙasashen biyu.

Gasar ta bana ta ƙunshi tambayoyi da amsoshi kan ilimin ƙasar Sin, da gabatar da jawabi cikin harshen Sinanci da sauransu, inda mahalarta gasar suka samu yabo matuƙa, duba da yadda suka iya harshen, gami da sha’awar da suka nuna wajen koyonsa.

Mai Fassarawa: Murtala Zhang