Matakan Amurka na kawo tsaiko ga ƙoƙarin duniya na kyautata yanayin kare haƙƙin ɗan Adam

Daga CMG HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, ta ce a ƙoƙarinta na kare muradunta na danniya, Amurka ta matse ƙaimi wajen yayata siyasantar da batun kare haƙƙin ɗan Adam, lamarin da ya kawo tsaiko ga ƙoƙarin kyautata yanayin kare haƙƙin dan Adam a duniya.

Kakakin ma’aikatar, Zhao Lijian ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na jiya, inda yake mayar da martani ga “rahoton kare haƙƙin ɗan adam na ƙasa na 2021” da Amurka ta fitar a baya bayan nan, wanda ya janyo suka da adawa ga wasu ƙasashe da dama.

A cewar Zhao Lijian, rahoton na Amurka, ya yi wasu tsokaci marasa kan gado game da yanayin haƙƙin dan adam a ƙasashe da yankunan duniya 198, amma kuma ya ware Amurka. Ya ƙara da cewa, zarge-zarge marasa tushe game da haƙƙin dan Adam da Amurkar ke yi, ba zai kyautata yanayin da ƙasar ke ciki ta fuskar haƙƙin ɗan Adam ba, yana mai cewa, abun da zai yi shi ne, bankaɗo munafurcinta da fuska biyu da take nunawa.

Mai Fassara: Fa’iza Mustapha