Ƙaramar Sallah: Sojojin Nijeriya, ku ruvanya ƙoƙarinku na kawar da ‘yan ta’adda, ya ishe ni goron Sallah – Babban Hafsah Sojojin ƙasa

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Hafsah Sojojin Ƙasan Nijeriya, (COAS), Laftana Janar Faruk Yahaya ya yi kira ga dukkan kwamandojin rundunar sojoji da su ƙara ruɓanya ƙoƙari wajen kawar da ‘yan ta’adda. Inda ya ƙara da cewa, babban goron sallar da yake tsammani daga gare su shi ne, su kawar da ɓata-gari, masu garkuwa da mutane, da ‘yan ta’adda masu yawan gaske. Sannan su ƙwato bindigogi da alburusai masu yawan gaske daga hannun ɓata-gari.

Laftana Janar Faruk Yahaya shi ya bayyana haka a cikin saƙonsa na Barka da Sallah ga dukkan kafatanin jami’an sojin Nijeriya.

Daraktan hulɗa da jama’a na jami’an sojin, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu a wani jawabin manema labarai ya bayyana cewa, COAS yana yabawa, kuma yana sane da irin sadaukarwa da jami’an suke wajen gudanar da ayyukansu a faɗin Nijeriya.

Haka, Shugaban jami’an sojin wasan kuma ya yi kira ga sojoji da su fake da wannan wata mai girma na Ramadhana don zama masu amana, biyayya, da kuma sadaukarwa. Ya ƙara da cewa, watan ya ba da dama mai kyau domin su ƙara tabbatar da ƙoƙarinsu na cika ayyukansa yadda kundin mulki ya buƙata daga gare su, sannan su ba maraɗa kunya a irin amanar da ‘yan Nijeriya suka ɗora musu.

Hakazalika, Janar Yahaya ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa jajantawarsa ta musamman ga jami’an sojojin da suka riga mu gidan gaskiya a bakin aikin bauta wa ƙasarsu kuma ya ce, iyalansu za su cigaba da samun tallafi da kulawa daga gare shi.

Haka COAS ya qara da cewa, a yanzu haka a ƙarƙashin shugabancinsa an ƙara inganta asibitoci da harkar lafiya na (asibitin sojoji) domin a cigaba da kula da iyalan sojojin da ma sojojin waɗanda suka ji raunuka sannan za a cigaba ɗaukar nauyin su da sauran abubuwa.

Sannan ya yi kira ga jami’an da su riƙe mutuncin ayyukansa su guje faxawa cikin harkar siyasa.

A ƙarshe, Janar Yahaya ya ce, yana fatan alkhairi da Barka da Sallah ga dukkan ‘yan Nijeriya sannan ya bayyana godiyarsa ga babban kwamandan rundunar sojojin ƙasar nan, Muhammadu Buhari da sauran ‘yan Nijeriya a kan irin haɗin kan da suke ba wa jami’an sojojin wajen gudanar da ayyukan su.