Ba ka da ɗa’a : Bafarawa ya mai da martani ga El-Rufa’i kan maganar dattawan Arewa

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Ɗaya daga cikin Dattawan Arewa, kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto a jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i sam ba shi da ɗa’a ko sanin ya kamata.

A cewar Bafarawa, a yayin da yake mayar da martani ga wata tattaunawa da El-Rufa’i ya yi da sashen Hausa na kafar yaɗa labarai ta BBC, inda shi El-Rufa’in ya bayyana dattaijan Arewa a matsayin akwai-ya-babu wato huhulahu waɗanda ba za su iya tabuka komai a zaɓe ba. A cewar sa, El-Rufa’i ƙaramin alhaki ne mai tunani irin na son zuciya.

A ciki tattaunawarsa da ‘yan jaridar, El-Rufa’i ya bayyana cewa, akwai wasu da suke a fadar shugaban ƙasa waɗanda suke ƙulle-ƙulle wajen taɗe ƙafar takarar Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugabancin Nijeriya a jamiyyar APC.

Bafarawa, wanda yana ɗaya daga cikin dattawan jam’iyyar PDP ya yi Allah wadai da wancan furucin na El-Rufa’i, wanda ya ƙasƙantar da matsayin dattawan Arewa ta hanyar bayyana cewa, gwamnonin jihohi Arewa guda 19 su ne ainihin dattawan Arewa.

“Rashin ta-ido ne da rashin ɗa’a ga wani ya furta hakan ga dattawan Arewa. Muna da dattawan masu mutunci da dattaku a Arewa, waɗanda suka damu da yankin da kuma ƙasar Nijeriya gabaɗaya”. Inji Bafarawa.

“Sam mutunci da dattakun mutum ba su da alaƙa da shekarunsa kamar yadda El-Rufa’i yake ta ƙoƙarin bayyanawa. A matsayinsa na ɗan shekaru 63 har yanzu yana cika bakin ya ci zaɓe. Mu mun sha cin zaɓe tun kafin ma ya san zai shiga siyasa, amma ba mu zo nan muna faɗar abubuwa na rashin kunya ba”.

Kuma ya ƙara da cewa: “Arewa ta fi ƙarfin wani mutum guda ɗaya da burinsa, kuma duk wanda ya kushe Arewa, zai gani a ƙoƙon shansa. Muna da nagartartun dattawa masu dattaku a Arewa, kuma muna alfahari da su. A cewar sa”.

Kuma a cewar sa, yana ba wa El-Rufa’i tabbacin cewa, za su ba wa APC mamaki a zavemai zuwa. Za su gane da Arewa da Nijeriya duk mallakinsu ce, a cewar sa.

Daga ƙarshe, Bafarawa ya sake bayyana cewa, Gwamnan na Kaduna ya sani sarai cewa, ‘yan Arewa ba za su taɓa zaɓar APC ba a zaɓe mai zuwa, amma duk da haka, yake yin shigo-shogo ba zurfi ga ɗan takarar na APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ta hanyar ba shi tabbacin zai samu nasara.

By Editor