Daga BASHIR ISAH
Ɗan jarida, Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian ta intanet, ya ce akwai haɗin baki game da matakin sauya fasalin wasu takardun Naira da Babban Bankin Nijeriya ya ɗauka.
Ya ce an ɗauki matakin ne don hana ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar (APC), Bola Ahmed Tinubu, cika burinsa.
Idan za a iya tunawa, kwanan nan aka jiyo Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya faɗa a hirar da tashar Channels TV ta yi da shi cewa, akwai wasu maƙiya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke ƙoƙarin ganin sun kai Tinubu ƙasa game da zaɓen 2023.
A martanin da ya yi a Tiwita game da zargin da Gwamnan El-Rufai ya yi, Jaafar ya ce Mamman Daura ba ya daga cikin maƙiyan Tinubun da ake magana.
Ya zayyano sunayen wasu da ya yi zargin suna yi wa ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, aiki.
“Na yi rubuce-rubuce da dama a kan irin tasirin da Mamman Daura ke da shi, amma abin mamaki ba ya daga cikin maƙiyan da ke ƙoƙarin kai Tinubu ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa.
“A lokacin da Osinbajo ya ziyarci Malam Mamman a gidansa a Abuja a Fabrairun 2022 don neman goyon bayansa dangane da aniyarsa ta takarar shugabancin ƙasa, inda ya tuna masa yarjejeniyar da ke ƙasa cewa Tinubu za a mara wa baya bayan saukan Buhari.
“Na fahimci ‘yan kan gaba wajen ƙin Tinubun a yau su ne; Shugaba Buhari, Sani Zangon Daura da Sabiu Tunde.
Yayin da Zangon Daura, ɗan shekara 85, yake mara wa Atiku a baya, shi kuwa Tunde yana jan zaren Buhari yana jujjuya shi a ɓoye.
“Zangon Daura, wanda tsohon minista ne a gwamnatin Obasanjo kuma fitacce a dattawan Arewa, ya sha alaƙanta kansa da PDP kafin Buhari ya lashe zaɓe a 2015.
“Sai ga shi Zangon Daura wanda na hannun daman Buhari ne ya bai wa jiga-jigan APC mamakin da ba su zata ba ta hanyar mara wa Atiku baya, bayan kuma ya ci gwamnatin APC na shekara takwas.
“Tunde ne aka yi zargin ya matsa wa Buhari lamba kan ya ba da umarnin sojoji su kare Emefiele daga kamun DSS. Majiyoyin cikin gida sun ce DSS ta nemi izini kotu don kamo Emefiele saboda aikata ba daidai ba ga fannin kuɗin ƙasa inda aka gano ya tallafa wa manmobin IPOB rancen kuɗaɗe.
Bayan haka, Emefiel ya bar ƙasar zuwa ƙetare da sunan hutun shekara, inda ya tabbatar da ya daidaita wa kansa hanya kafin dawowa ƙasar.
Ɗan jaridar ya ce ihun da gwamnonin APC ke yi ba don talakwa ba ne sai don yiwuwar samun nasarar jam’iyyarsu.
“Akwai abu ɗaya da yake a bayyane a wannan tirka-tirkar, matakin sauya fasalin Naira da Emefiele ya ɗauka na da nasaba da siyasa, haka ma zargin da DSS ke yi masa na yi wa kuɗin ƙasa ta’addanci.
“Yayin da yake jimamin rashin cim ma mafarkinsa na shugabancin ƙasa, Emefiele ya samu bayanin Tinubu ya tura kayan aiki zuwa jihohi.
“A nan ne Emefiele ya tuna cewa yanzu ne lokacin da ya dace Nijeriya ta sake fasalin kuɗinta. Sai kuwa ya shawarci Buhari a kan haka, Buhari ya amince masa ba tare da tuntuɓar Ministan Kuɗi, masana tattalin arziki, Majalisar Tarayya da sauran su ba.
“Ko a 2012, ƙorafe-ƙorafen jama’a ne suka taka wa CBN burki kan shirin sauya wasu kuɗaɗe da ya yi,” in ji shi.
