Rushewar gini: Minista ya sa a kamo masu ruwa da tsaki

Daga BASHIR ISAH

Ministan Birnin Tarayya, Malam Muhammad Bello, ya bai wa hukumomin tsaro umarni a kan su tsare jami’an Hukumar Gidaje ta Tarayya da injiniyan da ginin benen Abuja da ya rushe yake hannunsa.

Kodinetan Hukumar Buƙansa Abuja, Umar Shuaibu, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Asabar.

Ministan ya sa a tsare jami’an da ke da ruwa da tsaki wajen ba da izinin gina ginin da ya rushe da kuma injiniyan da ke aikin.

Shuaibu ya ce ginin wanda ya rushe a yankin Gwarinpa kwana biyu da suka wauce, mutum 24 suka maƙale yayin da uku sun riga mu gidan gaskiya.