Ƙarancin sabbin kuɗi: Zulum ya yi barazanar ƙwace takardar mallakar bankuna a Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi bankuna a jihar kan su bayar da sabbin kuɗaɗe a na’urorin cire kuɗi na ATM don rage ƙarancin kuɗaɗen ga jama’a, ya ce idan ba haka ba gwamnatin jihar za ta ƙwace takardun mallakar filayen bankunan; face sai idan bincike ya tabbatar cewa matsalar daga bankin CBN ce.

Zulum ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Juma’a a Maiduguri lokacin da yake rangadin rassan bankunan domin gane wa idonsa yadda ƙarancin takardun sabbin kuɗin ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali a jihar.

“Duk wani banki a Jihar Borno wanda ya ƙi loda sabbin kuɗi a ATM ɗinsa, kuma bai damu da halin da jama’a suke ciki ba, tare da ƙin zuba isasshen kuɗi domin sauƙaƙa wa al’ummarmu raɗaɗin da suke ciki ba, to za mu soke takardar mallakarsu nan take. Face bankunan da bincike ya nuna suna da wata matsala ta daban.” in ji Zulum.

Kafin wannan matakin, Gwamna Zulum ya nuna rashin jin ɗaɗinsa dangane da yadda ɗaruruwan jama’a ke yin dafifi a layukan ATM a bankuna domin cire sabbin kuɗaɗen.

“Kamar yadda kuke gani a nan, maras gata ne kawai zaka iya gani a kan layi; ban ga masu kuɗi a nan ba. Kuma an ce mutane da yawa suna nan tun ƙarfe 3:00 na asuba, wasu ko abinci ba su ci ba. Sannan kuma da sabbi da tsoffin takardun Naira ba a samu, kuma hakan na yin illa ga harkokin kasuwanci a jihar Borno, saboda jama’a su na shan wahala,” in ji Zulum.

Gwamnan ya ci gaba da cewa: “Yanzu mun saki albashin kusan Naira biliyan 5 amma bankuna ba su da kuɗi, wasu na’urorin ATM din ba sa aiki. Kuma ba mu da matsala da manufar CBN ko ƙa’idar cire kuɗi, sun ce kowane mutum zai iya cire 20,000 a wuni, to amma me ya sa ba kowa ne zai iya samun wannan N20,000 ba?

“A jiya ina garin Gubio mai yawan jama’a sama da 70,000 amma ba a iya samun Naira 100,000 a ɗaukacin karamar hukumar, da sabbi da tsoffin kudin duka. Misali ragon 100,000 yanzu bai wuce 35,000 ba, saboda yadda ake neman kuɗi, al’amarin da ya jawo miyagun masu hannu da shuni na zuwa ƙauyuka don cutar talakawa.” Inji Zulum.

Gwamnan ya buƙaci babban bankin Nijeriya (CBN) ya samar da sabbin takardun kuɗi a bankunan kasuwanci domin mutane su samu kuɗaɗensu.

“A yanzu haka a jihar Borno, na ziyarci na’urorin ATM a bankuna sama da goma amma babu kuɗi, mutane tsaye a layuka suna jiran tsammani.” in ji Gwamnan.