Masu neman kai ni ƙasa, nema suke a kafa gwamnatin riƙo, in ji Tinubu

“Nema suke su haifar da ruɗani a ƙasa don tilasta ɗage zaɓe”

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar shgabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, ya ce waɗanda suka ƙirƙiri ƙarancin mai da na sabbin takardun Naira, so suke su haifar da rikicin siyasa a kasa.

Tinubu ya bayyana haka ne a wajen gangami kamfe ɗinsa da aka gudanar ranar Juma’a a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.

Ya ce waɗanda ke da hannu cikin badaƙalar, nema suke ƙasar ta faɗa cikin matsin da zai haifar da ɗage babban zaɓen da ke tafe.

“Sun boye sabbin kuɗaɗen ne domin tunzara ku ku yi faɗa. So suke su haifar da ruɗanin da zai tilatsa daɗe zaɓe.

“Abin da suke buri shi ne ƙa samu gwamnatin riƙo, sai dai mun fi su wayewa. Ba za mu yi faɗa ba. Duk veran da ya sake ya ci maganin ɓewara, kashe kansa zai yi,” in ji Tinubu.

Haka nan, ya faɗa wa ’yan ƙasa cewar ya shiga takara ne domin kyautata rayuwarsu.

“Na shiga takara ne domin kyautata rayuwar ’yan ƙasa. Idan don abin da zan ci da kuma buƙatuna ne, Allah Ya hore mini,” a cewar Tinubu.