EFCC ta cika hannu da ‘yar Nollywood kan wulaƙanta sabbin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH

Jami’an Hukumar Yaƙi da Rashawa (EFCC) na shiyyar Legas sun fara binciken Oluwadarasimi Omoseyin wadda ‘yar fim ce a masana’antar Nollywood bisa zargin yin facaka da wulaƙanta sabbin takardun Naira.

EFCC ta ce abin da wadda ake zargin ta aikata ya saɓa wa Sashe na 21 (5) Dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN) na 2007.

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce an tsare Omoseyin ne a ranar Laraba a yankin Ikoyi, Jihar Legas.

Kamen nata ya biyo bayan bidiyon da aka yaɗa mai ɗauke da yadda take facaka da sabbin takardun Naira da tattaka su a wajen biki.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ‘yan ƙasa ke ci gaba da fuskantar matsin rayuwa sakamakon ƙarancin sabbin tarkadunna Naira.

EFCC ta ce za a gurfanar da ita bayan kammala bincike.