Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Amana dai tana da muhimmanci wajen tabbatar da adalci a tsakanin jama’a. Adalci a fasasrarsa a shari’a shi ne sanya kowane a inda ya dace da shi da miƙa haƙƙi ga mai haƙƙi. In an zo raba arzikin ƙasa a yi adalci. Duk dan ƙasa ya amfana da arzikin ƙasarsa daidai gwargwadon abun da ya dace da shi.
Matuƙar za a yi adalci to kusan kowa ko akasarin jama’a za su samu ingancin rayuwa. Akasin adalci shi ne zalunci. Duk wata ƙasa a duniya na buƙatar adalci don samun cigaba mai ma’ana. Aa tarihi mai zurfi an san labarun wasu shugabanni da a ka yi masu adalci da masu zalunci. Saboda illar zalunci an fi kanbama sunan shugabanni azzalumai.
Allah maɗaukakin Sarki ya bar gawar Fir’auna na zamanin Annabi Musa ya zama aya ga mutane. Bayan dubban shekaru har yanzu a na iya ganin gawar wannan Fir’auna wanda kan kashe ya kuma yi ikirarin rayawa. Hakanan har ya tava ba wa wazirin sa umurnin ya gina ma sa matakala ko sanya masa kuranga ko tsani don ya hau can sama ya je ya yi faɗa da Allah Mahaliccin Sammai da Ƙassai.
Ƙarshe Allah ya hallakar da shi a ruwa. Ina labarin Samudawa da Adawa da su ka zalunci na su? Ina ma’abota jefa mutane a rijiyar wuta? Ina masu cinikin bayi ta tekun Atatalantika da kuma ta hanyar Sahara? Duk waɗannan da na ambata sai tashin zan ce.
Babban muhimmin abu a rayuwar ɗan adam mai ƙarewa in bayan baya nan da shekaru masu yawa a riƙa tunawa da wani abu na alheri ba sharri ba. Abun da kan tabbatar da tarihi mai kyau shi ne adalci. Kamar nan Nijeriya har yanzu a na labarin shugabannin jamhuriya ta farko waɗanda wasu daga cikin su a ka kashe su amma an kasa kashe tarihi mai kyau da su ka bari.
Yayin da a ke la’antar waɗanda su ka kashe su, su kuma addu’ar alheri a ke yi mu su. Ba ma wani dogon lokaci a ka fauka bayan juyin mulkin 1966 a Nijeriya a ka samu gamawa da fitattun masu kisan gilla. Wato ma’ana in ma sun yi abun don su shantake ne a duniya su fora ƙafa ɗaya kan ɗaya, to hakan bai samu nasara ba.
Ƙaddara ma su na raye zuwa yanzu da dukkan su, sun haura shekaru 100- a duniya! Ko ba a mutu ba an shiga shekarun maida magani babban abinci. Wani abun dubawa a nan matuƙar shugaba ya yi adalci to ribar hakan zai bi shi har zuwa danginsa hakanan in ya yi akasin hakan to ban da shi ko dan sa a ka gani sai ka ga an yi tsaki ko ba a qaunar ganinsa.
Don haka ya na da matuƙar muhimmanci duk wanda ya samu dama musamman ta jagorantar al’umma to ya yi iya bakin ƙoƙari ya kaucewa son zuciya ya cika duk alqawuran da ya ɗauka ko ma dai aƙalla ya yi iya iyawarsa wajen yin adalci. Akwai wani bawan Allah da na gamu da shi a Gombe wanda ya kan yawaita kyauta da kuma nasiha cewa kowa ya zama mai gaskiya, amana da adalci.
Ya kan hana ’ya’yansa facaka da kuɗi amma ba ya hana taimako in an nema kuma ya kan raba duk abun da ya mallaka ga waɗanda ya sani da wanda ma bai sani ba. Na zanta da shi har na fahimci niyyarsa ta alheri ba kawai kan sa ya ke dubawa ba. Ya ce ya na fata ko ba ya raye idan wani na sa ya je neman wata alfarma to alherin da ya ke shukawa zai sa mutanen su mutunta jama’arsa.
Tuni ma ya ce wani ɗansa ya amfana da irin wannan alfarma a lokacin neman aiki da a ka ga cewa dan sa ne ta hanyar suna kawai sai a ka girmama shi kuma a ka yi ma sa abun da ya dace. Don haka ya ce in ka na da ɗan wani abu a aljihu kar ka ji kyashin taimakawa wani don abun da ka bayar shi ne n aka kuma matuƙar ka ba da kyauta da kyakkyawar niyya to abun da ka bayar zai dawo ta wata hanyar har ma a samu ninkin-ba-ninki.
Masu ruwa da tsaki da wasu ’yan Nijeriya a kusan kowane ɓangare na rayuwa na bayyana mabambantan ra’ayoyi kan mulkin shugaba Buhari a yayin da a ke ƙasa da mako biyu shugaban ya yi ban kwana da fadar Aso Rock. Tuni ma shugaban wanda ya nemi a yafe ma sa laifin da ya aikata ko duk wanda ya yi wa laifi ya yafe ma sa, ya koma wani gida a nan fadar da bisa al’ada shugaban da zai bar gado ya ke zama a kwanakin san a ƙarshe watakil don a samu damar gyare-gyare ko saite-saite ga gidan mulki na shugaban ƙasa mai shigowa.
Ra’yoyin sun shafi cika alƙawura ne ko akasin haka na mulkin Buhari a tsawon shekaru 8 da ya yi kan karagar mulki. Wasu ma kan haɗa har da wata 18 da ya yi a karagar mulkin a fadar Dodan da ke Legas zamanin mulkin soja. Masu kawo irin wannan misali na nuna takaicin yadda shugaban a soja ya hau karaga bayan kifar da gwamnatin farar hula yau kuma ga shi ya zama farar hula har ya ci gajiyar mulki sau biyu.
Kama daga alƙawarin samar da tsaro, samar da ayyuka ga matasa ko farfaɗo da tattalin arziki zuwa yaƙi da cin hanci da rashawa na daga abubuwan da mutane ke cewa shugaba Buhari ya taɓuka ko sam bai taɓuka ba. Gaskiya ra’ayoyin ba batun siyasa ko maganar addini da yanki. Mafi tsananin ra’ayoyin ma na fitowa ne daga bakin waɗanda su ka marawa shugaban baya tun fara takararsa ta siyasa a shekara ta 2003.
Musa Sarkin Adar wanda shaharerren ɗan majalisar wakilai ne kuma mai marawa shugaba Buhari baya ya ce in a ka duba tsantsar gaskiya an samu akasi da ya hana nasarar shugaba Buhari. Sarkin Adar ya buga misali da gwamnan babban banki Godwin Emefiele da ya zarga da cewa ya wargaza tattalin arzikin Nijeriya amma ba wani mataki da a ka ɗauka a kan sa. Hakanan yaƙi da cin hanci ma an zargi wasu da batun cin kuɗin makamai da sauran su amma maganar tamkar ta bi ruwa.
Shi kuma ɗan kasuwa Jauro Hammadu Saleh na cewa ya na takaicin yanda ya sa rai shugaban zai bunƙasa tattalin arziki amma ƙarshe bashi ke neman durƙusar da ƙasar. Ɗan kasuwar ya nuna damuwa yanda jibgin bashi ya taru a zamanin gwamnatin kuma kusan har ta na jajiberin tafiya amma ba ta haƙura da batun karɓo bashi ba.
Ɗan canjin kuɗi a Abuja Umar Garkuwa na da wani ra’ayin na daban da ke cewa duk ɓarnar da a ke zargin an tabka shugaba Buhari na sane kuma ya na ɗaukar matakai iya iyawar sa don daidaita lamura.
Tun hawansa karagar mulki, shugaba Buhari wanda ke tinƙaho da goyon bayan talakawa kuma har ma talakawa kan tarawa gudunmawa don ɗaukar nauyin kamfen; ya yi alwashin ba zai ci amana ba.
Shin shugaba Buhari ya ci amana ko bai ci amana ba; wa’adin mulkin sa ya zo ƙarshe kuma tarihi za a jira a ga irin adalcin da zai yi ma sa.
Ra’ayin jami’an gwamnatin Buhari ya sha bamban don su na nuna matuƙar nasara a ka cimma wai don ma gwamnatin Buhari ne da ba san yanayin takaicin da ƙasar za ta shiga ba ta fuskar taɓarɓarewar lamuran yau da kullum.
Gwamnatin Buhari ta yi nasarar magance kamuwa da ƙazuwa, tarin fuka da sauran cutuka a gidajen yari.
Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ya bayyana hakan a wajen buɗe wani ƙaramin asibiti na kula da cutar annoba a babban gidajn yarin Fatakwal da ke jihar Ribas kudu maso kudancin Nijeriya.
Aregbesola ya ce, ba kamar a baya ba, yanzu gwamnati ta samar da yanayi mai kyau a gidajen yari da ma samar da wajajen kula da kiwon lafiyar ‘yan yarin.
Rahoton ya ƙara da cewa ministan ya bugi ƙirjin gwamnatin na kashe maƙudan kuɗi kan kowane ɗan gidan yari da su ka kai Naira miliyan ɗaya ga kowanne wajen ciyarwa da kula da lafiya.
Injiniya Buba Galadima ya shawarci shugaba Buhari da ya ƙaura zuwa wata aasa nesa daga Nijeriya da zarar ya sauka daga karagar mulki.
Buba Galadima wanda ya shahara da lamuran hamayya, na magana ne a wata muhawara kan nasarori ko akasin hakan da shugaba Buhari ya cimma a mulkinsa na tsawon shekaru 8.
Galadima ya ce, a matsayin sa na wanda ya san shugaba Buhari ciki da bai ya ce matuƙar ya zauna a cikin Nijeriya zai iya ganin wani abun bacin rai daga wani daga waɗanda ya fifita kan muƙamai da hakan zai iya sanya shi matuƙar damuwa.
A nan Buba Galadima ya ce, maimakon shugaba Buhari ya koma Daura, Kaduna ko ma zama a Abuja, ya dace ya fice can ƙetare don ya huta da takaici.
Kammalawa;
Komai ya yi farko to zai yi ƙarshe in ban da ikon Allah da ba shi da farko bare ƙarshe. Don haka duk abun da mu ke yi a rayuwar duniya mu shuka alheri don a na yi wa alheri kirari da gadon barci.