Babbar Sallah: Dakarun tsaro sun tabbatar da yin sallar idi cikin aminci a Arewa maso Gabas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaron Atisayen Haɗin Kai (OPHK) da ke aiki a ƙarƙashin atisayen DESERT SANITY V/SIEGE a arewa maso gabashin Nijeriya, sun cimma gagarumar nasara a sassan shiyyar sakamakon tabbatar da gudanar da sallar Idi cikin aminci yayin fuskantar matsin ayyukan ‘yan ta’adda.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran jami’an haɗaka na OPHK, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar a yau Laraba, ya ce dakarun da aka tura ƙauyen Ngoshe a Jihar Borno, sun tabbatar da bada wadataccen tsaro wajen yin aiki tare da ‘yan bijilante da wasu ‘yan sa kai daga mazauna yankin, lamarin da ya bayar da damar gudanar da sallar cikin walwala da lumana.

Wannan ci-gaba na zuwa ne a daidai lokacin da yankin ke fuskantar matsalolin barazanar ‘yan ta’adda, wand ya sa aka yi ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Haka ma dakarun Task Force Brigade na 26 a ƙarƙashin OPHK, waɗanda suka tabbatar da walwalar jama’a a yayin Idi a garin Gwoza ta hanyar ƙarfafa matakan tsaro tare da gabatar wa al’ummar yankin addu’o’in fatan na gari daga manyan jami’an sojoji.

A wani labarin kuma, Laftanal Kanal Uba ya bayyana cewa, dakarun na OPHK sun yi nasarar daƙile wani hari a ƙauyen Gar Gwigwi da ke Ƙaramar Hukumar Biu yayin da aka cafke mutane uku da suka haɗa da Aliyu Mamadu, Umar Mohammed da kuma Adamu Aliyu, wanda sun kasance suna addabar ‘yan garin.

Daga cikin ababen da aka ƙwato a hannunsu akwai wayoyin hannu, agogunan hannu, layu, barandami, tsabar kuɗi da wata bindigar toka da aka gano ta wani mamban ƙungiyar Miyetti Allah mai suna Mallam Manu Ibrahim ce da aka yi fashi kwana guda kafin kamen.

A ƙarshe, ya jaddada ƙoƙarin dakarun na daƙile dukkan nau’ukan ayyukan ta’addanci a shiyyar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa acikin al’umma.

By Babaji