Babu wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Filato da bankin JAIZ – Gwamna Lalong

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos

Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa game da sake gina ƙonanniyar Babbar Kasuwar Jos, cewa gwamnatin Filato za ta bai wa Bankin JAIZ damar amfani da kasuwar har tsawon shekaru 40 har sai bankin ya cire kuɗinsa na aikin sake ginin.

Gwamnan ya sake jaddadda cewa, ko da an sake gina kasuwar Hukumar Kula da Babbar Kasuwar Jos ce za ta cigaba da tafiyar da harkokin kasuwar, kuma daga kuɗaɗen da ake tattarawa daga hayar shagunan da za a biya shi ne za a biya bankin da shi, inda bankin zai ɗauki kashi 60 gwamnati kuma karɓi kashi 40.

Lalong ya bayyana haka ne yayin da yake ƙaddamar da aikin gina wasu rukunin gidaje 800 da gwamnatin jihar za ta samar wa ma’aikatan jihar, wanda za a gina a ƙauyen Rafiki da ke yankin Ƙaramar Hukumar Bassa.

Ko a yayin wani babban taron masu ruwa da tsaki na jiha, da gwamnatin jihar ta kira, Gwamna Lalong ya tabbatar musu da cewa Babbar Kasuwar Jos za ta cigaba da kasancewa ƙarƙashin gwamnatin Jihar Filato, aikin sake ginin sabuwar kasuwar ne kawai bankin JAIZ zai ɗauki nauyin gudanarwa.

Ya ce, gwamnati ta daɗe tana ƙoƙarin ganin ta sake gina kasuwar, inda ta yi ta tallata buƙatar masu son zuba jari a kasuwar daga ciki da wajen Nijeriya, waɗanda suka yi ta bayyana sharuɗɗa masu tsauri, da gwamnati ba za ta iya biya ba, har sai da bankin JAIZ ya zo da nasa tayin cewa, za su sake gina kasuwar da kuɗinsu, gwamnati fili kawai za ta bayar.

Gwamnan ya nuna ɓacin ransa sakamakon irin yadda ake amfani da addini wajen haddasa rashin kwanciyar hankali a jihar, don cimma burin siyasar wasu, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wasu masu shirin mayar da hannun agogo baya a zaman lafiyar da jihar ta samu ba.

Sauran wakilan al’umma da suka haɗa da sarakunan gargajiya, tsofaffin ‘yan siyasa da ‘yan majalisun jiha da na tarayya, da malaman addini, waɗanda suka bayyana goyon bayansu ga wannan shiri da suka ce zai ƙara dawo da martaba da kwarjinin Jihar Filato ta fuskar kasuwanci da zuba jari, sun buƙaci gwamnati ta cigaba da fahimtar da jama’a muhimmancin aikin da yadda tsarin zai gudana, don a kawar da jita-jitar da take yawo a tsakanin jama’a.