Fadar Shugaban Ƙasa ta koka bisa kisan dabbobinta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Fadar Shugaban Nijeriya ta bayyana damuwarta bisa kisan da ake wa namun dajin da ke cikin gandun dajinta a baya-bayan nan.

Mahukunta Fadar Aso Rock, sun bayyana hakan ne ta bakin Sakataren Gidan Gwamnati, Tijjani Umar, a yayin da yake karɓar tawagar masu kula da Gandun Daji Na Ƙasa tare da takwarorinsu a Fadar Shugaban Ƙasa, waɗanda aka fi sani da ‘Royal Rangers’.

Umar, wanda ya jaddada muhimmancin kariya da kiyaye tsirrai da dabbobi a muhallansu na asali, ya kuma yi alƙawarin inganta yanayin kiyaye muhalli ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace na kiyaye namun daji.

Bugu da ƙari, ya ce za a ɗauki matakan da suka dace domin kare yanayi da kuma mayar da nau’ukan namun daji da tsirrai da aka yi asararsu a fadar gwamnati.

Ya sanar da cewa, an keɓe wasu wurare a Fadar Shugaban Ƙasa domin zama muhalli ga wasu nau’ukan namun daji.

Namun dajin a cewarsa sun haɗa da biran tantalus da kadoji da ƙaton kunkuru da manyan macizai da ɓerayen daji da zabbi da jemagu da nau’ikan tsuntsaye iri-iri, waɗanda an keɓe musu wurarensu.

Ya kuma yi kira ga ma’aikata da masu ziyarar fadar da su guji cutar da halittun, inda ya ƙara da cewa za a kafa alamomi a wasu wurare domin wayar da kan jama’a kan bin ƙa’idojin da suka dace, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Umar, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ta hannun Daraktan Yaɗa Labarai, Abiodun Oladunjoye, ya taya Royal Rangers da sauran takwarorinsu na Nijeriya murnar zagayowar Ranar Masu Kula da Gandun Daji ta Duniya ta bana, wanda aka yi a ranar 31 ga watan Yuli.