Dole sojoji su yi bayani kan maƙudan kuɗaɗen da muka ba su – Osinbajo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin Shugaban Nijeriya Yemi Osinbajo ya buƙaci sojojin ƙasar da su yi wa jama’a bayani a kan irin maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ta ba su domin gudanar da ayyukan tsaro a ƙarƙashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Osinbajo ya ce jama’ar ƙasa na da hurumin sanin irin maƙudan kuɗaɗen da wannan gwamnati ta ware domin tunkarar matsalolin tsaron da suka addabi Nijeriya wanda ke kai wa ga rasa dubban rayuka, don kore shakku dangane da yadda gwamnati ke fuskantar ƙalubalen tsaro.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce abin takaici ne kowanne lokaci idan an yi maganar tsaro, sai ka ji wasu sojojin na cewa ba su da kayan aiki.

Saboda haka ya dace ma’aikatar tsaro ta gabatar da wani tsari wanda zai dinga bayyana irin kuɗaɗen da su ke kashewa a ɓangaren tsaron.

Osinbajo ya bayyana cewar ya dace a ce Nijeriya ta shawo kan matsalar ‘yan bindigar da ake fama da ita ta wajen nuna ƙwarewa da kuma nuna dabarun yaƙi.

Jaridar Daily Trust ta gabatar da wani bincike a kan kasafin kuɗin tsaron da aka bai wa ma’aikatar tsaro tun shigowar gwamnatin Buhari a shekarar 2015 kamar haka:

2015 an ware musu Naira biliyan 968; 2016 Naira tiriliyan guda da miliyan 700; 2017 Naira tiriliyan guda da miliyan 1,500; 2018 kuma Naira tiriliyan guda da miliyan 1, 350; sai 2019 Naira tiriliyan guda da miliyan 1, 400.

Haka zalika 2020 aka ba su Naira triliyan guda da miliyan dubu 800. Yayin da 2021 kuma Naira tiriliyan guda da miliyan dubu 960 da kuma kasafi na musamman Naira biliyan 722 da miliyan 530.