Bana dai Allah ya raka taki gona, amin

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gaskiya wannan addu’ar a bana ta na da matuƙar muhimmanci, don yadda takin zamani ya yi ɗan karen tsada. Duk da manufar Allah ya raka taki gona ta na nufin ko oho ba abin da zai faru, musamman a ce in mutum ya fita daga wannan ƙungiyar zuwa waccar ko daga wannan jam’iyyar zuwa waccar da sauran misalai. In a ka yi fassarar kai tsaye da ita ce manufar rubutun nan, za a amsa da amin summa amin don duk wanda ya samu wadataccen taki a gonarsa a bana zai yi murna ainun.

Ƙalubalen da ya ke damun manoma a jihohin Arewa da dama a shekarun nan shi ne na rashin tsaro inda mutum zai iya shiga daji wasu su sace shi ko ma in kwanan sun qare shi kenan. Bana kuma an samu ƙarin ƙalubale na wannan tsada ta fitar hankali. Na ji wasu na hira cewa, akwai takin da ya doshi Naira 30,000! Mai ƙaramin albashi in ya dage ya sayi buhu ɗaya ba zai samu na sayen kayan miya ba a watan sai ƙarewa da buge-buge.

Tun farkon gwamnatin nan ta shugaba Buhari ta ɗauki matakin ƙarfafa komawa noma don shi ne dahir tsakanin akasarin ‘yan Nijeriya. Cikin matakan har da ba da lamuni da kayan noma. Shin shirin ya yi nasara ko kuwa a’a za a fi ganewa daga farashin kayan abinci a kasuwa. Tsadar kayan abinci ka iya zama har da tsadar farashin taki, iri da magungunan feshi. Kazalika ba kowa ne daji ba ne a ke iya shiga a noma. Manyan manoma kuma kan noma su adana abincin a manyan ɗakunan ajiye abinci. Wasu ‘yan kasuwa kuma kan shiga har gona su saye abincin tun yana ɗanye su ɓoye sai in ya yi matuƙar tsada su fitar su sayar. Ka ga ya nuna laifin ya shafi sassa da dama.

A ƙaddarama ga abinci nan a kasuwa jingim, amma kuma ya gagari akasarin jama’a saya. Kun ga a nan gwamnati ba ta cimma burin ta na ƙarfafa cewa a koma noma don wadata ƙasa da abinci ba. Masu azancin zance kan ce kwai a baka ya fi kaza a akurki. Ma’ana duk yawan abinci mai daɗi ga ɗan karen tsada gara wanda ya ke hannun talakawa duk ƙarancinsa.

Na ji daga wani gwamna na ɗaya daga jihohin da ke tinƙaho da noma na cewa bana taki zai gagari ƙananan manoma kuma ya nuna zai yi wuya taki ya isa gona. Mu na magana kan takin zamani NPK, UREA da sauran su. Idan kuma har taki ba zai samu zuwa gonakin talakawa da kan yi amfani da kwai a baka ba, ba shakka za a iya samun matsala na yiwuwar ƙara tsadar abinci. Idan talaka zai ɗan noma abinda zai ci ya raka shekarar har kusa da damina, za a samu sauƙi don buƙatar abincin a kasuwa zai zama ba yawa. A gefe guda matuƙar manyan manoma ne su ka yi noman, akwai yiwuwar jinkirin isar abincin kasuwa.

A lokacin da abincin zai shiga kasuwa zai zama akwai matuƙar buƙatarsa. Matuƙar buƙatar wata haja a kasuwa a tsarin ilimin saye da sayarwa, kan sa tashin gauron zabi na farshin kaya. Yayin da manyan manoma su ka sayi taki da tsada su ka noma abinci, babbar riba za su nema. Wannan na nuna binciko dalilan da su ka saka taki matuƙar tsada da kuma hanyoyin da za a bi wajen samar da shi ko da kuwa raba shi lamuni za a yi ga jam’iyyun gama kai na manoma. Hakan ma ya kamata ya buɗe bincike ko cusa ilimin dabarun noman zamani da zai sa a riƙa noman ko ba ma wadataccen takin zamanin. Akwai wanda na ga ya na ɗibar jujin anguwarsu ya na kai wa gona.

A shekarun baya da a ke da tsaro a kan samu makiyaya su yi mashekasri a gonaki inda a kan samu taki daga kashin shanu kuma hakan kan sa a samu yavanya mai yawa. Yau hakan na da wuya don an samu rikicewar dazuka inda makiyayan ma ba su da shanun ko ba su da zaman lafiyar zama a wasu dazukan. Gaskiya sai an ɗauki sabbin matakai da su ka haɗa da ita kan ta gwamnati ta shiga harkar noman inda za ta riƙa noma ko karve amfanin gona daga manoman da ta rabawa kayan aiki ta biya su haƙƙinsu sannan sai ta adana abincin. Da zarar an samu ƙarancin abinci sai gwamnati ta buɗe ma’ajiyunta, ta sayar da abincin kan farashin da aljihun talaka zai iya saya.

Rufe kan iyaka da gwamnatin nan ta shugaba Buhari ta yi a baya da hana shigo da musamman shinkafa ya kawo yawaitar manoma shinkafa. Su kuma manoman kan yi alfahari da abin da su ka noma. Ƙungiyar manoman ma da ke haɗe da gwamnati kan shirya taron nuna dalar shinkafa. An yi hakan a arewa maso yamma da kuma a baya-bayan nan a Abuja. Duk da dai wasu mutane da mu ka zanta da su ’yan jihar Kebbi na cewa akwai shinkafar da a kan shigo da ita daga ƙetare da a kan ce a Nijeriya a ka noma ta.

Hakan ya saɓa da yunƙurin da hukumar kwastam ta ke yi na yaƙi da simoga. Manoman na shinkafa gabanin samun ƙalubalen dakatar da zuwa aikin hajji kan zama cikin masu iya biyan kujerar Makkah don yadda su ke samun ribar noman da su ke yi. Kazalika a duk lokacin da wani ya buƙaci a buɗe iyakar don shigo da shinkafar ƙetare, manoman kan nuna damuwa cewa a na neman yi mu su kafar angulu a aikin da su ke yi na sama wa ƙasa shinkafar da ’yan ƙasa ke buƙata. Ina amfanin baɗi ba rai.

Ko ma ta yaya a ka samar da shinkafar, matuƙar talaka kan yi amfani da kusan duk kuɗin da ya mallaka wajen saya ai ba wani sauƙi da a ka samu. Masu neman a bar kaya su na shigowa daga ƙetare na cewa yin hakan zai taimaka wajen samun gasa a tsakanin shinkafar gida da ƙetare. Ƙara inganta ta gida ta hanyar tsince tsakuwa da kuma rahusar ta, zai sa a ƙarshe mutane su koma sayen ta gidan kaɗai su manta da ta ƙetaren.

Idan za a tuna lokacin zanga-zangar ENDSARS wasu sun fake da tsadar abinci wajen kai hari kan rumbunan abinci na gwamnati da kwashe abincin har ma da takin zamani. Wannan ya afku a sassa daban-daban na Nijeriya. Yanayin fasa rumbunan gwamnati na abinci har sai da ya iso yankin Abuja bayan hakan ya zama ruwan dare a wasu jihohi da masu ɗibar kayan ke ɗaukar hakan a matsayin ganima.

Lamarin a lokacin ruɗanbin na EndSARS ya wuce tunkarar kayan abinci, don a Abuja har takin zamani a ka wawashe.

Bayan lafawar akasin an tabbatar da asarar rayuka a babbar wawar da a ka yi a Abuja a garin Gwagwalada inda mutane su ka yi dafifi da fasa rumbun abinci da ya jawo turereniyar da ta haddasa rasa rayuka da samun raunuka. Hakan ya nuna an yi ta’annatin ta hanyar in b aka yi ba ni waje har a take mutum ya mutu don a samu a yi wuf da buhun taki ɗaya tak!

Alhaji Halliru Auta, Basaraken Doshin Paikon Kore ne a yankin Gwagwalada da ya bugi jaki da takin ta hanyar nuna ko ma za a ɗebi kaya kar su wuce na abinci. Don ya fahimci cewa ko gwamnati ba za ta yi dirar mikiya kan ’yan ƙasa masu neman lomar tuwo ba. Halliru Auta wanda limamin masallacin Gwarawa ne da a idon sa a ka wawashe kayan, ya buƙaci gwamnati ta riqa kula da walwalar al’umma. Ita kuma walwalar ta shafi hatta samar da taki da sauran kayan noma cikin farashi mafi rangwame ko ba da lamuni na gaskiya da gaskiya.

Hakanan ya zama gwamnatin ta na zuba ido don tabbatar da waɗanda ke cin gajiyar lamuninta sun cancanci samun lamunin don kar a wayi gari a ba wa wani lamunin noma a gaya sayo babur ko tsohuwar mota da kuɗin. Wani ma zai iya fente gidan sa ya ɗinka babbar riga ya hakimce ko da na ’yan kwanaki ne ya ɗana.

Gwamnatin birnin Abuja ta zayyana waɗanda su ka fasa rumbunan da cewa masu aikata laifi ne don ita tuni ta kammala raba kayan tallafin annoba. Ma’ana duk wanda ya ɗauka kayan tallafin annoba ne ya wawashe to ba lalle hakan ba ne.

Alhaji Abbas G. Idris shi ne shugaban hukumar agajin gaggawa na Abuja da ke cewa sun rubuta rahoton duk tallafin da a ka bayar.

A yanzu dai akwai alamun gwamnati da sauran cibiyoyin adana abinci a Abuja na sauyawa kayan abinci wajen zama don gudun masu warwaso.

Kammalawa:
Ga dai damina ta sauka ko ta na daf da sauka a garuruwan da a ke noma ga taki kuma ya zama sai mai tarin sulalla. Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin da lamarin ya shafa ya dace su duba wannan lamari da idon basira don samar da mafita. Hakan kuwa ko zai sa gwamnati ta ƙara tura kuɗi sashen taki ta hanyar samar da rangwame zai taimaka ainun wajen koma wa gona da kwarin gwiwa ko ba ƙwarin zuciya.