Bankin Duniya ya tallafa wa manoman 620 a Nasarawa

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya fara rabon wani tallafin kuɗi wanda Bankin Duniya ya raba wa manoma 620 a juhar waɗanda aka zaƙulo su daga yankunan karkara 10 a faɗin jihar.

Da yake jawabi a wajen rabon tallafin wanda aka gudanar a garin Doma, hedikwatar ƙaramar hukumar Doma a jihar, Gwamnan ya ce raba wa manoman kuɗaɗen yana daga cikin ƙudirin Gwamnatin Tarayya ne tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya na ci gaba da taimaka wa manoma a jihar don inganta fannin noma da zummar samun wadataccen abinci.

Ya ce, ita ma gwamnatin sa a kwanan nan ta raba taraktocin noma guda 23 wa manoman da ingantaccen shuki don bunƙasa sha’anin noma a jihar.

Sule ya bayyana cewa, shirin bai da rancen tallafin za a ci gaba kuma za a riƙa biya ne ba tare da riba ba don ana yi ne saboda agaza wa manoman baki ɗaya a jihar.

Ya ce, waɗannan manoma daga yankunan karkara 10 ɗin da suka amfana a wannan karo sun fito ne daga ƙaramar hukumar Toto da Doma a jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewa, ba shakka canjin yanayi da ake fuskanta a yanzu ya jawo babban matsala ga muhalli da ma rayuwar manoma baki ɗaya inda ya bukaci a cigaba da shirin don magance ƙalubalen.

Da take jawabi, shugabar tawagar da suka raba tallafin ga manoman, Dr. Joy Iganya-Agene ta bayyana cewa, cibiyar ta ACReSAL ta raba wa kimanin manoman 620 ne waɗanda maza 367 ne sannan 253 mata.