Daga BASHIR ISAH
Bayan shafe watanni takwas ba ya aiki, jirgin saƙan Abuja-Kaduna ya fara aiki a ranar Litinin.
Jirgin ya dakatar da aiki ne tun wata takwas da suka gabata sakamakon harin ‘yan bindiga.
Manhaja ta kalato cewa, an ga fasinjoji na shiga jirgin a tashar Idu cikin tsattsauran tsro a safiyar Litinin.
Sai dai ba a samu tururuwar fasinja ba kamar yadda aka saba gani a baya a lokacin da jirgin ke loadin safe a tashar ta Idu.
Manhaja ta gano an ɗauki matakan tsaro da dama, ciki har da kafa kyamarorin CCTV a sassa daban-daban domin sanya ido a kan zirga-zirgar jirgin da masu shigar sa.
Haka nan, an bai wa ƙa’idar nan ta amfani da Lambar Shidar Ɗan Ƙasa (NIN), wajen shiga jirgin.
Da suke yi wa jaridar Daily Nigerian bayani, wasu daga cikin fasinjojin sun bayyana farin ciki da gamsuwarsu da dawowar jirgin bakin aiki.
