NAF ta kashe ’yan ta’addan da ake nema ruwa-a-jallo a ƙauyukan Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jiragen yaƙin Rundunar Sojin Saman Nijeriya sun kawar da wasu jiga-jigan ’yan ta’addan Zamfara guda bakwai da ake nema ruwa-a-jallo.

An kawar da ’yan ta’addan ne da suka yi ƙaurin suna a Jihar Kaduna sakamakon harin da jiragen yaƙin sojojin saman Nijeriya biyu suka kai musu.

An tattaro cewa, waɗanda aka kashe sun haɗa da Jibrin Gurgu, Isah Jauro da Tambowal daga jihar Zamfara. Sauran da aka kawar sun haɗa da Noti, Bala, Yunusa da Burti wanda ya kasance sanannen abokin wani ɗan ta’adda da ake nema ruwa-a-jallo, Haladu Buharin Yadi.

Wani jami’in leƙen asiri na tsaro ya shaidawa manema labarai cewa, farmakin da ya yi sanadin kashe ’yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, rundunar sojin sama na Operation Whirl Punch ne suka kai farmakin a maɓoyar ’yan ta’addan da aka gano a unguwar Alhaji Ganai, Sabon wurin Buhari da Dogon Maikaji duk a cikin ƙaramar hukumar Giwa.

Ya ce, “an aiwatar da hare-haren ne sakamakon sahihan bayanan sirri daga majiyoyi masu inganci kan ayyukan ta’addanci a yankin baki ɗaya.

“Saboda haka, an ba da izinin kai hare-haren ne a ranar 1 ga Disamba 2022. An kai hare-hare ta sama a kan ‘yan ta’adda da kuma yankunan Tsofa da Riyawa a Igabi da Birnin Gwari a Jihar Kaduna.”

A cewar jami’in, bayanan da aka samu sun kuma nuna cewa ’yan ta’addan sun yi mummunar ɓarna sakamakon ruwan wuta da aka yi musu.

Ya ce, “Tun daga lokacin da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Sam Aruwan ya tabbatar da wannan harin ta sama, a wata sanarwa da ya fitar a ranar 2 ga Disamba, 2022, ya bayyana cewa, harin da sojojin sama suka kai sun gano tare da tarwatsa sansanin ’yan ta’adda 8 tare da kuɓutar da mutane 10 da aka yi garkuwa da su”.

Air Commodore Edward Gabkwet, mai magana da yawun NAF, ya tabbatar da harin da jiragen nasu suka kai.

Ya godewa ’yan Nijeriya bisa goyon bayan da suke bai wa NAF da sauran jami’an tsaro, waɗanda ke taimaka wa nasarorin da sojojin Nijeriya suka samu a kan ’yan ta’adda a baya-bayan nan.

A cewarsa, “Dawowar ’yan gudun hijirar zuwa gidajen kakanninsu da miƙa wuya na ’yan ta’adda sama da 10,000, da iyalansu, musamman a cikin watanni 3 da suka gabata a Jihar Borno, da kuma yadda ’yan Nijeriya ke da damar yin tafiye-tafiye cikin walwala. Titin Kaduna zuwa Abuja, da sauran hanyoyin da har ya zuwa yanzu masu hatsarin gaske na daga cikin alamomin da ke nuna cewa haƙiƙa ƙoƙarin jami’an tsaro yana samun sakamako mai kyau.”

A ɗaya ɓangaren kuma, Manyan hafsoshin soji a hedikwatar tsar, da wasu kwamandojin ayyukan soji daban-daban a ƙasar sun nemi fahimtar sojoji kan rashin biyan su alawus-alawus na tsawon watanni biyu.

Duk da rashin biyansu, sojojin na cigaba da gudanar da ayyukan kakkaɓe ’yan ta’adda da masu zagon ƙasa ga tattalin arziki a wuraren daban-daban na faɗin ƙasar.