Benzema ya koma Al-Ittahad ta Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Karim Benzema ya koma Al-Ittihad kan yarjejeniyar kaka uku, in ji wata majiya daga ƙungiyar ta Jeddah, wadda ta sanar da kamfanin dillacin labarai na AFP.

Ranar Lahadi Real Madrid ta sanar cewar tsohon ɗan wasan Faransa mai shekara 35 zai bar Santiago Bernabeu, bayan shekara 14 da ya yi a Sifaniya.

Idan har ta tabbata cewa Benzema ya koma Saudiyya, to zai taka leda tare da tsohon ɗan ƙwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo mai wasa a ƙungiyar Al Nassr.

Ronaldo ya koma Saudiyya da taka leda daga Manchester United a watan Janairun 2023, bayan da aka kammala gasar kofin duniya a Ƙatar.

Ana alaƙanta Lionel Messi da cewar shima zai koma taka leda a gasar ta gabas na tsakiya, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris Saint-Germain a ƙarshen kakar nan.

Manyan jami’an Al Hilal ta Saudiyya sun je Faransa, domin ƙulla yarjejeniya da Messi, in ji wata majiya da ta sanar da AFP.

Benzema ya koma Real Madrid a 2009 daga ƙungiyar Lyon mai buga Ligue 1.

Ya buga wa Real wasa 648 da cin ƙwallo 354, shine na biyu a yawan ci wa ƙungiyar ƙwallaye a tarihi, bayan Ronaldo.

Tsohon ɗan wasan tawagar Faransa, ya lashe Champions Leagues biyar da La Liga huɗu da Copa del Rey uku a Real Madrid.

Bayan da ɗan wasan ya ja ragamar Real Madrid a 2021-22 da ta lashe Champions League ya kuma ɗauki Ballon d’Or, daga nan ya yi ta jinya da ta hana shi buga wa ƙasarsa kofin duniya a Qatar.

Benzema ya yi ban kwana da Real Madrid ranar Talata.

Kawo yanzu Saudiyya ta lissafa ‘yan wasa 10 fitattu da take son su buga gasarta nan gaba, waɗanda ko dai sun ci Champions League ko sun ɗauki kofin duniya.

Cikin ‘yan ƙwallon har da Luka Modric na Real Madrid da golan Tottenham, Hugo Lloris da , N’Golo Kante na Chelsea, waɗanda kwantiraginsu ke daf da ƙarewa.

Ita dai Saudiyya na fatan samun izinin karɓar baƙuncin gasar kofin duniya a 2030 ko kuma 2034, domin ta bunƙasa tamaula a faɗin ƙasar.