Buhari ya kori manajan NIRSAL saboda zargin sa da almundahana

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauke Manajan Daraktan Hukumar ba da Agajin Ibtila’i da Tallafin Noma (NIRSAL), Aliyu Abdulhameed, a kan zargin yin almundahana.

Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban qasar ya kori Abdulhameed daga aiki a yammacin ranar Alhamis 2, ga watan Disamba 2022, inda aka fatattake shi daga ofishin nasa jim kaɗan bayan nan.

Abdulhameed dai ana zarginsa da laifin karkatar da wasu kuɗaɗen hukumar tun daga lokacin da aka naɗa shi muƙamin a shekarar 2015 zuwa yau.

Haka zalika, rahotanni sun sake bayyana cewa, a halin yanzu tuni gwamnatin ta baza komar neman madadinsa.

Wata majiya ma ta bayyana cewa, an ƙwace dukkan ababen hawan ma’aikatar da suke a hannunsa. Inda ya tafi gida a wata ƙaramar Bilhodi.

A watan Yunin 2022, ne dai kafafen yaɗa labarai suka bankaɗo yadda Abdulhameed ya karkatar da wasu kuɗaɗen hukumar har Naira biliyan guda. Wanda ya yi amfani da asusun shugaban sashen kula da kuɗi na hukumar, Idris Issa Aweda, domin ɓad-da sawu.

Aweda na amfani da asusun banki har gida uku, wato FCMB (4986133010) da GTB (0245155058) da kuma bankin Stanbic IBTC (0021195810) don amsar wa Abdulhameed kuɗaɗen cuwa-cuwarsa.

Sannan an kama shi da amfani da NIRSAL duk da ba hukumar tsaro ba ce ba. Inda ya nemi a ba wa hukumar kuɗin kayan kare kai, kamar mota mai sulke da sauran makamai, a cewar sa saboda barazanar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya musamman a gonaki.

Haka nan, ya sallami shugaban sashen binciken kuɗi, Mista Olalekan Olusanya da Olusola Omole a ƙoƙarinsa na ɓoye badaƙalar miliyoyin Nairori da kuma magance sa idonsu a kan cuwa-cuwar da yake aiwatarwa.

Kazalika, an samu Abdulhameed da yin sama-da-faɗi da kuɗaɗen da gwamnati ta ware don shigo da alama a ƙasar nan a yayin da ƙaranci da tsadar fulawa ya yi ƙamari a ƙasar.

NIRSAL dai hukuma ce ta da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya samar domin tallafa wa kasuwancin da suka shafi noma a Nijeriya.

A sakamakon almundanar Abdulhameed ne ma ya tilasta wa CBN ya hana kuɗin gudanarwa ga hukumar NIRSAL a shekarar da ta gabata.