Ɗalibi Aminu ya kawo ƙarshen faɗansa da Aisha Buhari bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Yanzu dai ya tabbata fadan da ke tsakanin matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, da ɗalibin nan Aminu Mohammed Adamu, ya ƙare.

Hakan ya biyo bayan ganawar da Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi da Aminu ɗin ne bayan da aka sako shi daga gidan maza.

Aminu, wanda ɗalibi ne a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa, ya gamu da fushin Aisha ne bayan da ya caccake ta a shafinsa na Tiwita inda ya ce ta ci kuɗin talakawa ta yi ɓul-ɓul.

Lamarin da ya sanya jami’an tsaro na DSS suka bi sawun ɗalibin har makarantarsu suka damke shi inda suka ɗauke shi zuwa Abuja.

Rahotanni sun ce Aminu ya ɗanɗani kuɗarsa a hannun jami’an tsaron, wanda daga bisani aka maka shi a koto kan zargin da ya yi wa matar Shugaban Ƙasa.

Kama ɗalibin ya haifar da ce-ce-ku-ce ciki da wajen ƙasa, inda wasu ke ganin matakin da Aisha ta ɗauka bai dace ba duk da dai ɗalibin ya yi rashin ɗa’a.

Daga bisani Aisha ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibin, inda ta ce ta janye ƙarar ce sakamakon manyan ƙasa sun sa baki cikin batun, kamar dai yadda lauyanta ya faɗa.

Bayan sake shaƙar iskar ‘yanci, Aminu Adamu ya sake shiga shafinsa na Tiwita inda ya wallafa saƙon ban-haƙuri dangane da sukar da ya yi wa Aisha, da kuma nuna godiya ga ‘yan ƙasa dangane da alhinin da suka nuna a lokacin da aka kama shi.

“Ina son yin amfani da wannan damar wajen neman afuwar wadanda na bata wa, musamman uwarmu, A’isha Buhari. Ban yi haka don bata muku rai ba, kuma Insha Allahu zan canza in zama mutum na gari, ina godiya da afuwarki, Mama,” in ji Aminu.