An tallafa wa wanda lakarsa ta tsinke da miliyan N1 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Ƙaramar Hukumar Buji a Jihar Jigawa, ta ba da tallafin Naira miliyan ɗaya ga wani matashi da ya samu matsala a lakarsa sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi kwanan baya.

Tallafin ɓangare ne na ƙoƙarin da ƙaramar hukumar ke yi wajen ganin ta inganta rayuwar nakasassu da marasa lafiya a yankin.

Matashin, Ahmad Karanjau, ya haɗu da tsautsayin ne a kan hanyar Abuja zuwa Benin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Abdullahi Sulaiman Yayari, ya tabbatar da cewa Hukumar Buji za ta ci gaba da tallafa wa Ahmad wanda a halin yanzu yake kwance a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

Da yake jawabi a madadin ‘yan uwa mara lafiyan, Malam Abubakar Karanjau, ya yaba da tallafin da shugaban ƙaramar hukumar ya bai wa ɗan uwansa.

Ya ƙara da cewa, tallafin zai taimaka musu matuƙa wajen ci gaba jinyar mara lafiyan.