‘Yan bindiga sun buɗe wuta cikin wani masallaci a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

‘Yan bindiga sun yi dirar mikiya a wani masallaci dake garin Maigamji a Ƙaramar Hukumar Funtua a dai-dai lokacin da ake gabatar da Sallar Issha’i.

Wani mazaunin garin ya shaida wa majiyar Manhaja cewa, da zuwan ɓarayin ana tsaka da Sallah sai suka buɗe wuta inda nan take suka harbi mutane biyu ciki har da wanda rahotanni suka ce shi ne limamin dake jan Sallar.

Wanda yanzu haka suna karɓar magani a babban asibitin garin funtua.

Rahotannin dai sun bayyana cewar, maharan sun yi awon gaba da mutane da dama.

Harin na zuwa ne bayan an ɗan samu sauƙin hare-haren ‘yan bindigar a wasu sassan yankin na ƙaramar hukumar ta funtua.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina ba ta yi ƙarin haske ba kan lamarin.