Buhari ya taya sabbin shugabannin APC murna

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi taya murna a hukumance ga sabbin zaɓaɓɓun shugabannin jam’iyyarsu ta APC ƙarƙarshin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, su 79 da aka zaɓa yayin babban taron jam’iyyar da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata a Abuja.

An zaɓi sabbin shugabannin ne don su daidaita wa jam’iyyar APC zama tare da tabbatar da cewa jam’iyyar ta kai ga hayewa tudun mun tsira yayin babban zaɓen 2023.

Cikin sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, Buhari ya ce yadda taron nasu ya gudana cikin nasara hakan ‘yar manuniya ce kan irin gagarumar nasarar da APC za ta samu yayin zaɓen baɗi.

Kazalika, sanarwar ta ce taron ya nuna yadda Shugaba Buhari ya samu nasara wajen haɗa kan ‘yan jam’iyya wajen rabon muƙamai.

Haka nan cewa, nasara ce ga masu zaɓe a Najeriya wanda a yanzu suka samu yaƙinin samun sabon shugabancin ƙasa a 2023.

Sanarwar ta ƙara da cewa nasarar taron APC kunya ce ga maraɗa, musamman idan aka yi la’akari da yadda ‘yan hamayya suka yi ta yaɗa labarai kan cewa taron ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Ta ci gaba da cewa, bayan da ya tabbata cewar gaskiyar APC ta danne shirin ‘yan PDP shi ya sa suka kasa nutsuwa suka shiga kafafen yaɗa labarai suna yaɗa bayanan ƙarya don neman cimma burinsu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, nan gaba APC za ta gudanar da zaɓen fid da gwani inda za a zaɓi waɗanda za a bai wa tutar tsayawa takara na muƙamai daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *