Buhari ya yi Allah wadai da kisan lauya Omobolanle Raheem a Legas

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da kashe wata lauya da ’yan sanda suka yi a ranar Kirsimeti a Jihar Legas.

Buhari ya ce, ya yi matuƙar kaɗuwa da kisan Omobolanle Raheem, tare da bai wa hukumaomin ‘yan sanda umarni kan ɗaukar matakin da ya dace a kan waɗanda suka yi aika-aikar.

Shugaban ya ce, wannan manuniya ce kan yadda ake mu’amala da bindigogi ba yadda ya dace ba.

Ya ƙara da cewa, faruwar al’amarin fargarwa ce ga hukumomi ciki har da hukumar ‘yan sanda kan aiwatar da tsare-tsaren da ake da su dangane da mu’amala da bindigogi da kare ‘yancin ‘yan ƙasa.

“A wannan lokaci na alhini, ƙasa na tare da ‘yan uwan marigayiyar da Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, (NBA).

“Ina mai tabbatar da za a yi adalci kan wannan batu,” in ji Buhari.

A ranar Lahadin da ta gabata wadda kuma ta kasance ranar Kirsimeti aka kama wani ɗan sanda mai muƙamin ASP bisa zarginsa da kisan wata lauya kuma mai harkar gidaje, Bolanle Raheem, a Jihar Legas.

A yayin da lamarin ya faru dai, ɗan sandan na tare da wasu abokan aikinsa su biyu a unguwar Ajah da ke jihar.

Bayanai sun nuna cewa Bolanle na tare da wata ’yar uwarta da ’ya’yanta su huɗu, lokacin da suke ƙoƙarin ficewa daga wani wajen cin abinci, a lokacin da ɗan sandan ya bindige ta a ƙarƙashin gadar Ajah.