Fifita ƙwarewa a kan shaidar gama karatu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Muhawara game da wanda ya fi muhimmanci tsakanin ƙwarewa kan wani fannin rayuwa ko fasaha, da ingancin shaidar kammala karatu, ba yau aka fara ba. An daɗe tsakanin manazarta, masana harkokin koyarwa, da masu nazarin cigaban rayuwa suna bayyana ra’ayoyin su game da abin da ya fi dacewa ana bai wa fifiko, don ya dace da cigaban rayuwa da ake samu.

Tambayar da akasari aka fi yi ita ce, wanne tsarin koyarwa ya fi dacewa da zamani? Wacce manufa ake da ita wajen koyar da ilimi? Wacce rayuwa ake so ɗaliban da ke karatu a manyan makarantun ilimi za su yi bayan sun kammala karatun su na Jami’a ko Kwalejojin Kimiyya da Fasaha, da sauran cibiyoyin ilimi.

A yayin da wasu ke ganin mutum ya shiga makaranta, ya yi jarabawa, ya samu shaidar kammala karatu, shi ne ginshiqin samun kowanne ilimi, wasu na ganin samun shaidar karatu don kawai ɗalibi ya cika wasu sharuɗɗa na makaranta ko ya shafe tsawon wasu shekaru yana koyon wani fanni na ilimi, bai wadatar ya zama mai ilimi ba, matuƙar abin da ya koya ba ya iya aiki da shi don inganta rayuwar sa ko ta wasu.

A Nijeriya ba sabon abu ba ne ka ga wanda ya karanta ilimin harkokin gona ko zana taswirar ƙasa da gine gine, yana aiki a banki, aikin jarida ko dai wani aikin ofis na wata ma’aikata, inda sam aikinsa bai shafi karatun da ya yi ba. Abin da aka fi mayar da hankali kawai shi ne an kammala makaranta an samu shaidar kammala Digiri ko makamancinsa, za a je a nemi aiki da kwalin karatu, ko ma wanne iri ne. Abin da wasu ke ƙorafi a kai shi ne wasu darussa ko kwasa kwasan da ake koyar da su a makarantu suna buƙatar kwaskwarima, ko sabunta fasalinsu, don su dace da cigaban rayuwa da canjin zamani.

Wasu kwasa-kwasan da ake koyarwa a manyan makarantun qasar nan, ba su da wadatattun takardun karatu ko kayan gwaji, sai dai dogon turancin kawai ake koya musu daga tsofaffin takardun koyarwa, ko kuma su ɗaliban su haɗa kuɗi su nemi kayan gwaji su koyawa kansu, don samun shaidar kammala karatu, ba tare da sun samu gogewar da ta kamata ba.

Ga shi kuma an haifar da wata gasa ko kishi tsakanin ɗaliban jami’o’i da na kwalejojin kimiyya da fasaha, inda ake ganin martabar digiri fiye da ta Babbar Diploma ta Ƙasa (HND). Alhalin makarantun koyar da sana’o’i da ƙere-ƙere su ne suka fi mayar da hankali wajen koyar da ilimin da ɗalibai za su iya riƙe kansu har bayan makaranta.

A shekarar da ta gabata wasu ɗalibai da ke shekarar ƙarshe ta karatunsu na digirin farko a sashin nazarin koyar da ilimin injiniyancin ƙere-ƙere a Jami’ar Jos, sun ƙera wata ƙaramar mota samfurin motocin tsere da suka sanyawa suna Espera, domin samun shaidar kammala karatunsu na sashin Injiniyanci.

Amma abin takaicin shi ne, ɗaliban ba su iya haɗa komai a ɗakinsu na gwaje-gwaje da ke Jami’ar ba, sai da suka je kamfanin wani mai ƙere-ƙere kafin suka iya ƙera motar da suka gabatar da samfurinta.

Waɗannan ɗalibai misali ne na irin halin da ɗaliban ke fuskanta a ƙasar nan, saboda akasari karatun da suke yi na karatu ne kawai ake koya musu a aji ba a haɗawa da gwaje-gwajen da za su tabbatar da ingancin karatun da suka yi. Abin da ya sa wasu ke tunanin ba sa buƙatar sai sun yi karatu mai zurfi ko digiri, matuƙar suna ganin suna da basirar ƙirƙirar wasu abubuwa da ƙwarewar da suke da ita. Sai dai a ƙasa kamar a Nijeriya inda ake fifita shaidar kammala karatu abu ne mai wuya, mutum ya samu aiki ko wani tallafi ba tare da shaida ba.

Abin da masana ke faɗa shi ne, koyar da ilimin da zai bai wa ɗalibi damar yin tunanin sarrafa wani abu ko ƙirƙira da za ta kawo canji ko cigaba a rayuwar jama’a, ta hanyar aiki da ilimin da ya koya da taimakon malaminsa. Ilimin da zai mayar da ɗalibi ya zama kadara da al’umma za ta amfana da iliminsa shi ne muhimmin abin da yanzu zamani ke nema, shi ne kuma sabon tsarin koyarwar da wasu ƙasashe suke runguma, don koyar da ‘yan ƙasashen su da ma ‘yan wasu ƙasashen kamar Nijeriya, inda sai ‘ya’yan masu hali ne kawai suke samun wannan damar.

Ko da yake mu a nan Nijeriya ba mu ba da muhimmanci ga wannan tsarin ba, amma mahukunta a Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa ta fitar da wani tsari da zai inganta yadda ake koyar da ilimin kimiyya da fasaha da kuma ƙirƙira a makarantu, tun daga matakin firamare zuwa jami’a, da kuma darasin koyar fara sana’a da buɗe kasuwanci, tsarin da a gajarce ake cewa, STEAM.

Domin Gwamnatin Tarayya ta lura cewa, bayan ba za ta iya samar wa dukkan ‘yan ƙasa ayyukan yi ba, haka kuma ta lura da yadda talauci da rashin ayyukan yi ke barazana ga cigaban ƙasar nan. A saboda haka gwamnati ke ƙoƙarin ganin an samar da horo da kayan aiki ba kawai don koyar da ɗalibai ba, har ma da horar da malaman da suke koyar da ɗaliban ta yadda za su samu sauƙin koyarwa cikin wannan sabon tsarin.

A, sakamakon wannan sabon sauyi, masana harkokin ilimi na ganin hatta tsohon tsarin yadda ake koyarwa, malami a gaban aji shi ma ya kamata a sauya shi. Abin da ake so shi ne a samar da tsarin yadda ɗalibi da malami za su yi aiki tare wajen ƙirƙiro wani abu, da sarrafa shi a aikace, ba tare da dogon turanci ba.

Wannan na nuni da cewa, idan har gwamnati za ta mayar da tsarin makarantun ƙasar nan bisa irin wannan salon koyarwar, tare da inganta yanayin muhallin koyarwa za a samu canji a yanayin ingancin ilimin da ake koyarwa, da kuma irin matasan da suke kammala karatu, ta yadda ba za su gama karatu su zama nauyi a wuyan gwamnati ba.

Ilimin sana’o’in ko kasuwanci, da suka shafi sarrafa kwamfiyuta, noman zamani, kafinta, gyaran waya da gine-gine, adin kwalliyar mata da girke-girke, duk za su samar da matasa masu dogaro da kai da ilimi mai gina al’umma. Har wa yau ƙalubale ne kan gwamnati ta farfaɗo da makarantun ta na koyar sana’o’i da ƙere-ƙere, don cimma manufar gwamnati na sauya akalar koyarwa da yaƙi da rashin ayyukan yi.

Ko da yake babban ƙalubalen da ake fuskanta a ƙasar nan, ba rashin sanin dabarun aiki ko mai ya kamata a yi ba ne. A’a, rashin mayar da hankalin ‘yan siyasa da masu mulki ne kan abubuwan da suka shafi raya ƙasa da cigaban jama’a. Don haka yanzu da gwamnati ta waiwayo wannan ɓangaren ya kamata a yi da gaske don ganin an ɗauki matakan da suka dace na kawo bunƙasar ilimi da amfani da bai wa yawan matasa masu ƙwazo da muke da su, don kawo cigaban masana’antu da ƙere-ƙere.