Irin jawabin da ya kamata Buhari ya yi a game da noma a Nijeriya

Daga: NAFI’U SALISU

A kwanakin bayan mun ji yadda Shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi wasu kalamai dangane da ‘yan Nijeriya da suke kokawa a kan halin yunwa da matsin rayuwa da ake ciki, wanda mafi yawan mutane kalaman ba su yi musu daɗi ba, duba da yanayin da ake ciki na ƙunci da wahalar rayuwa.

“…Babu wani dalilin da zai sa ‘yan Nijeriya su yi kukan yunwa…” in ji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a cikin maganganunsa a kwanakin baya.

To sai dai a hange da nazari na adalci, ko kusa ko alama wannan kalmar ba ta da daɗi, kuma ba ta cancanci shugaban ƙasa ya faɗe ta ga ‘yan Nijeriya ba, domin duk dalilinsa dai bai wuce a kan maganar a je a
yi noma ba. Tun yaushe ake yin noman, kuma ana yi ba a daina ba. Amma menene ya jefa ƙasar cikin mawuyacin halin da ake ciki a halin yanzu? Da wannan ya duba sai ya ga ina ne matsalar take, kuma ya za a magance ta cikin sauƙi da zai fi a kan wancan furucin da ya yi?

“…idan mutum yana jin yunwa ya tafi gona ya yi noma, ga ƙasar noma nan Allah ya ba mu…” inji shugaba Muhammadu Buhari a cikin kalaman nasa.

Ko shakka babu Nijeriya muna da ƙasar noma a ko’ina, birni da ƙauye. To sai dai akwai tarin matsalolin da suka daɗe suna addabar su manoman. Kuma mafi akasarin manoman ƙasar nan talakawa ne, waɗanda suka sadaukar da rayukansu domin su noma abinda za su ci da iyalansu, kuma da shi suke gudanar da harkokinsu na rayuwar yau da kullum. Waɗannan talakawa sun daɗe suna shan wahala wajen aikin gona, kuma wasu da yawa shi ne sana’arsu tun kaka da kakanni, har kawo yanzu.

Abinda nake so shugaba Muhammadu Buhari ya sani shi ne, da a ce bai kasance shugaban ƙasa a yanzu ba, kuma baya cikin Gwamnatin da ke mulki, to na tabbatar ba zai iya zuwa ƙauye ya yi noma ba saboda ƙalubalen da manoma suke fuskanta a halin yanzu. Na sani cewa ya nuna damuwarsa a kan a yi noma don a ciyar da ƙasa da abinci, wanda ƙila hakan ne ya sa ya ɗauki matakin rufe iyakokin ƙasar nan don a daina shigo da kayan abinci da wasu kayayyakin. To ina son yin tambaya a kan haka, shin hakan ya sa abincin ya wadata a Nijeriya? Idan ya wadata ɗin, to me ya sa yake da tsada? Mu dubi wannan abin da idon basira da kyakkyawan tunani.

A yanzu haka akwai jihohin da manoman suke cikin tashin hankali a Arewacin ƙasar nan dangane da noman da suka yi bana. Bayan jarrabawar da Ubangiji ya saukar a kan samun lalacewar amfanin gona, sai kuma rashin samun damar iya zuwa gonar da wasu talakawan suke yi saboda fargabar ‘Yan ta’adda (masu garkuwa da mutane).

Wannan shi ne babban dalilin da ya hana wasu talaka yin noma a wannan mulkin na Buhari. Ba a maganar tsadar kayan gyaran gonar ma, irin su taki, injinan huɗa, maganin feshi da sauransu. A cikin waɗannan jihohi akwai; Kano, Katsina, Zamfara, Sokoto, Giwa da Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Na ziyarci wasu daga cikin waɗannan jihohi, kamar Kamfanin Doka da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna, inda a bana ɗin nan mutane da dama ba su iya samu sun yi noma ba, sai da suka bayar da hayar gonakinsu domin su ci abinci. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon tsadar takin zamani, da magungunan feshi, balle uwa-uwa injinan huɗa.

Tunda yanzu babu shanun huɗa, saboda idan kana kiwon tinkiya ko rago ma ba ka da kwanciyar hankali a wannan yanki balle kuma shanu. Ko gadar shanun ka yi a gurin mahaifinka to tilas ne ka rabu da su, idan kuma ba haka ba, har gida za a zo a kore su kana ji kana gani, wataƙil ka iya tsira da ranka idan ba a ɗauke ka an yi daji da kai an nemi kuɗin fansa ba. Don haka dole suka haƙura, domin a farashi mafi ƙaranci da za ka samu injin huɗa shi ne dubu ɗari shida (N600,000).

Don Allah wanne talaka ne yake da kuɗin siyan wannan da Damina? Ko kuma a ce za ka sayi buhun taki a kan kuɗi N28,000 ko mafi ƙaranci N25,000. A daminar nan ta bana, da kuma lokacin kakar nan da ake cire amfanin gona, a garin Kamfanin Doka, na ga mutane da dama waɗanda tsoron ‘yan ta’adda ya sa suka riƙa ciro farin wakensu tun yana ɗanye bai gama ƙosawa ba suna kawo shi gida. Domin idan ba su cire shi a hakan ba, to makiyaya (kamar yadda ake cewa) za su tura dabbobinsu cikin gonar sun cinye shi tas.

Haka nan itama Dawa bata gama ƙosawa ba aka riƙa yankota ana kawo ta gida, wata ma sai dai a bai wa dabbobi, domin ba ta ko gama ƙosawa ba ballantana ta bushe. Akwai mutumin da ya shuka wake mai yawa, waken ya yi ‘ya’ya sosai gwanin sha’awa, amma kuma duk bai ƙosa ba ɗanye ne tushe da ‘ya’yan, amma haka makiyayan nan suka ce sun ba shi kwana biyar ya ɗebe shi ko su zuba shanunsu.

Ya ce musu su yi haƙuri waken bai ƙosa ba, suka ce ya cire shi a haka da ganyen ya baiwa dabbobinsa na gida idan yana so, idan kuma baya so shi kenan. Wallahi haka mutumin nan ya zuba mutane aka taru aka cire waken bai ƙosa, ya kuma biya waɗanda suka taya shi cirewa. Shin me ake so wannan mutumin ya yi fyace zuciyarsa ta buga ko ya rataye kansa? Idan ɗaya daga cikin haka ta faru me za a kira hakan? Cigaban noma a lokacin mulkin Buhari, ko cigaban ta’addanci?

Haka kuma na ga mutumin da tun daga nan Kano ya sa aka nema masa wuri a jihar Kadunan a wannan yanki na Doka domin ya bi umarnin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, na kiran da ya yi a koma gona. Amma a ƙarshe noman da aka yi masa bayan kuɗi mai yawa da ya kashe, shi ma abinda aka noman an tura shanu sun cinye, a ƙarshe sai buhu guda aka samu.

Wai a hakan ma shi ya yi sa’a, domin akwai maƙwabtansa da suke da gonaki a kusa da shi, wani an shuke masa buhun farin wake, wani kuma na waken suya, amma kowannensu babu wanda ya cire ko tushe ɗaya, duk waɗannan makiyaya sun cinye. Hakazalika, wani Bagobiri ɗan jihar Sokoto da ke zaune a wannan gari, shi ma sun cire masa masara tas!

Ire-iren waɗannan fa ba za su lissafu ba a cikin wannan rubutu, domin suna da matuƙar yawa. Hakazalika, a yankin Dutsimma a jihar Katsina, mutane da dama ba su iya noma gonakinsu ba saboda barazanar ‘yan bindiga. Wani mutum da ya yi noma a yankin Dutsin-ma, sai da ‘yan bindiga suka sa ya biya su Naira miliyan ɗaya domin ya cire amfanin gonarsa.

Bayan ya biya kuɗin, ya ɗebi ‘yan aiki ya kai su gonar amma aka zo har gonar aka kwashe su aka yi garkuwa da su, aka kira ‘yan uwansu aka ce sai kowa ya biya kuɗin fansa. Sannan a jihar Kano, a ƙaramar hukumar Munjibir, makiyaya sun shiga gona wani bawan Allah suna yi masa varna ya yi musu magana, a take suka kashe shi. A jihar Zamfara da Sokoto kuwa yankunan da manoma suka yi asara a sakamakon ‘yan ta’adda, masu fakewa da kiwo suna ta’addanci, varnar da suka yi wa manoma ba ƙarama ba ce.

Abinda mutanen ƙauye talakawa suke nomawa ba ya isarsu su ajiye su ci har wata shekarar ta zagayo, balle kuma ga hidimomi na bukukuwan aurar da ‘ya’ya, da sauran wasu hidimomi waɗanda suka gaza yiwuwa da rani ko bazara sai idan kaka ta zo mutanen ƙauye sun kawo amfanin gonarsu gida.

Shin shugaba Buhari ya san cewa da yawan mutanen qauye sai da kaka ne suke iya aurar da ‘ya’yansu mata a wannan lokacin? Ko kuma su yi wa ‘ya’yansu maza aure? Shin shugaba Buhari ya san cewa wasu mazan a ƙauye idan an yi musu haihuwa suna jingine yin suna sai lokacin kaka? Saboda rashin wadatar da za su yi hidimar suna a lokacin bazara?

Maganar gaskiya shugaban ƙasa Buhari bai shirya shirin yadda za a yi noma a samar da wadataccen abinci a ƙasar nan ba, idan kuma ya yi, duk shirin da ya dace ya yi don ciyar da qasar nan abinci har a fitar da shi wasu ƙasashen, to akwai lauje cikin naɗi a cikin shirin. Domin ya kamata manoman da suke ƙauyuka su sami kariya ta kowacce fuska. Samun kariya daga harin ‘yan bindiga, samun kariya daga cinye amfanin gona daga makiyaya, samun sauƙin takin zamani, da maganin feshin gona, da dukkan wani kayan aikin gona.

Gwamnati tana da kuɗin da za ta yi duk wannan, a ko’ina a cikin qasar nan. Hakazalika, tana da jami’an tsaron da za ta baza su a ko’ina, tare da na’urorin zamani da za su iya gano duk wata maɓoya ta ‘yan ta’adda. Idan duk a Gwamnatin nan an yi wannan, me ya sa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba zai fito ya sanar da ‘yan ƙasa cewar ya yi duk abinda ya kamata ya yi ba, sannan ya faɗi inda matsalar take. Amma saɓanin hakan sai ya riƙa fitowa yana gaya wa mutanen ƙasa kalamai masu ɗaci waɗanda za su iya tunzura al’umma, ko a riƙa tsinuwa da alawadai a game da mulkinsa.

Ni ina ganin cewa, kamata ya yi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fito ya ce: “Mutanen Nijeriya ina godiya da ku ka zave ni na zamo shugaban ƙasa a shekarar 2015, har lau dai a shekarar 2019 kuka sake zaɓa ta. Mun yi ƙoƙarin cika alƙawurran da muka ɗaukar muku na samar muku da kyakkyawar rayuwa a cikin kyakkyawan yanayi, amma Allah bai nufa ba sakamakon har yanzu al’amurra ba su daidaita ba.

“Mun rufe iyakokin ƙasa domin a yi noma a samu wadatar abinci a ƙasa, shi ma wannan shirin mun yi iya bakin ƙoƙarinmu, amma har yanzu akwai ƙalubale. Mun sani ‘yan ƙasa suna fama da yunwa da matsin rayuwa, amma sannu a hankali komai zai warware. Ni shugaba Muhammadu Buhari da abokan aikina a cikin wannan Gwamnati tamu, ina mai ba ku haƙuri.”

Da irin waɗannan kalaman shugaba Muhammadu Buhari ya yi ga ‘yan ƙasa, ina mai tabbatar da cewa da masoyansa sun ƙaru, kuma da an yi masa uzuri. Hatta Allah (Maɗaukakin Sarki) sai ya faɗi kyakkyawan sakamako ga bayinSa kafin ya faɗi narkon azaba. Idan kuma ya faɗi narkon azaba, to a gaba zai faɗi kyakkyawar sakayya da ni’ima. Amma a duk mafi yawan kalaman shugaba Buhari yakan yi su ne ba a cikin yanayin tausayawa ga ‘yan ƙasa ba, wataƙil rashin iya tafiyar da shugabanci ne yake kawo haka ga wasu shugabannin al’umma.

Shi shugaba a duk inda yake, duk rintsi duk wahala ba ya duba kansa da abinda yake so, sai ya fara duban al’ummar da yake shugabanta da abinda suke so. Haka nan duk lokacin da ka zamo shugaba, to ka sani cewa nauyin al’ummar da yake kanka ba zai ba ka damar ka ce za ka yi bacci cikin farin ciki ba, ko za ka ci ka sha a cikin farin ciki ba, har sai ka saka farin ciki da walwala ga al’ummarka. Don haka, ya kamata shugaba Muhammadu Buhari ka fito ka sake wasu kalaman ga ‘yan Nijeriya, amma ba irin waɗancan na bayan ba. Kalaman neman afuwa dangane da gazawarka a mulki, yin hakan shi zai sa a iya kiranka da shugaba tsayayye kuma adali.

Nafi’u Salisu
Marubuci/manazarci
[email protected]
[email protected]
08038981211

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *