Gobara ta ƙone gidaje a Legas

Daga BASHIR ISAH

Al’uma mazauna yankin Ebute Metta a Jihar Legas sun shiga hali na jimami da alhini sakamakon gobarar da ta auku a yankin ranar Talata da safe.

Rahotanni sun ce, gobarar ta ƙone gidaje da dukiya mai mai yawa.

An ce gobarar ta fara ne daga wani gida sannan ta faɗaɗa zuwa maƙwabta.

Wani ganau ya ce, “Da misalin ƙarfe 9:05 na safe na kira Hukumar Kwana-kwana inda jami’ansu suka isa wurin bayan minti 40.

“Cinkoson jama’a da ya haɗu a wurin ya haifar da jinkiri, domin sai da ‘yan sanda suka taimaka kafin ‘yan kwana-kwanan suka samu gudanar da aikinsu,” in ji majiyar.

Ko a ranar Litinin an samu aukuwar makamancin haka a yankin Ikosi Ketu da ke jihar.

Da take bayani, Shugabar hukumar, Adeseye Margaret, ta ce an samu aukuwar gobara sau 24 a ranar Kirsimeti kaɗai a jihar, wanda hakan shi ne iftila’in gobara mafi yawa da aka taɓa fuskanta cikin sa’o’i 24 a faɗin jihar.