Majalisa ta amince wa Buhari ƙarin kasafin biliyan N819

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dattawa ta amince da ƙarin kasafin biliyan N819 da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata don cike giɓin kasafin 2022.

wannan na zuwa ne bayan da Majalisar ta ƙara wa’adin aiwatar da kasafin na 2022 zuwa ranar 31 ga Maris, 2023.

Da farko dai Majalisar ta amince da tiriliyan N17.12 a matsayin kasafin 2022, daga bisani ta ƙara kasafin zuwa tiriliyan N17.31 bayan da Shugaba Buhari ya buƙaci hakan inda ya ce tasirin yaƙin Ukraine da Rasha ga tattalin arzikin ƙasa ya haifar da buƙatar ƙarin.

A ranar Laraba Majlisar ta amince da kasafin bayan da shugaban kwamitin rabon kasafi, Jibrin Barau, ya gabatar da rahotonsa ga zaman haɗin gwiwar da Majalisar ta yi.

A rahoton nasa, Jibrin ya ce, manufar ƙarin kasafin ita ce don magance matsalolin da ambaliyar ruwa ta haifar a 2022 da kuma samun halin kammala ayyukan da suka kai kashi 85 da aiki.

A makon da ya gabata Shugaba Buhari ya gabatar wa Majalisar ƙarin kasafin domin neman amincewartwa.