Burin mu al’ummar Kano su samu ci gaba a gwamnatin Abba Gida-Gida – Lawan & Sons

Daga MUHAMMAD MUJITTABA A Kano

An bayyana cewa al’ummar Kano masu kishinta da son ci gabanta babu wani abu da suke buƙata daga sabuwar gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf wato Abba Gida-Gida domin ita Kano cibiya ce ta kasuwanci da noma, ilimi da sarauta sune ginshiƙai da Kano ke tafiya akan su a shekara da shekaru, don haka duk wata gwamnati da ta zo burin al’ummar Kano a samu cigaban kasuwanci da sauran fannoni na rayuwa da Kano ta ke kan su.

“Don haka babban burinsu a cewarsu shi ne gwamnatin Abba ta samar musu da abubuwan cigaban al’ummar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Lawan Ibrahim Mai Kafet & Sons a birnin Kano a ranar Litinin da ta gabata.

Haka kuma ya ƙara da cewa ‘yan kasuwa, malamai, manoma, sarakuna, da sauran al’umma akwai buƙatar su bai wa wannan gwamnati haɗin kai ta hanyar shawarwari da addu’o’i na alkairi domin a ga Kano ta cigaba da samun zaman lafiya da ƙaruwar arziƙi, “wanda burinmu shi ne gwamnati da mu da sauran al’ummar kowa ya samu nasara akan abun da ya sa a gaba wanda shi ne nasarar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.”

A qarshe Alhaji Lawan & Sons ya yi kira da waɗanda a ka zaɓa tun daga kan ɗan majalisar jiha na wakilai da sanatocin Nieriya da Shugaban Ƙasar Nijeriya Alhaji Asiwaju Ahmad Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da sauran masu ruwa da tsaki da kowa ya sa Nijeriya a gaba fiye da kowacce buƙatunsa na qashin kansa domin ta haka ne za a samu ci gaban tsaro da zaman lafiya, bunƙasar noma, lafiya, tattalin arziƙi da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *